Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar ƙwararren ɗan jarida, Kabir Yusuf

Spread the love


Daga USMAN NASIR KAROFI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Kabir Yusuf, wanda ya rasu ranar Talata.

Bayanin hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kakakin Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, a yau Laraba.

Sanarwa ta ce, “Yusuf ƙwararren ɗan jarida ne, wanda ya kasance manemin labarai na Birnin Tarayya na Jaridun The Triumph da kuma Radio France Internationale Hausa.

“Ya yi wakilin Fadar Shugaban Ƙasa na jaridu da dama tsawon shekaru da dama har zuwa rasuwarsa.

“Shugaba ya yi addu’ar Allah ya jikan sa, kuma ya ba iyalansa hakuri a wannan lokacin baƙin ciki da kuma kullum.”

Kabir Yusuf ya rasu ne a wayewar garin Laraba bayan gajeriyar jinya a gidansa da ke Kano bayan dawowarsa daga aikin hajjin bana.

By ukarofi