Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Barau Jibrin ya miƙa ta’aziyyar rasuwar ƙwararren ɗan jarida Kabiru Yusuf.
Sanarwar ta fito daga bakin mai bashi shawara, Alhaji Ismail Mudashir. Ya jaddada cewa marigayin mutum ne mai jajircewa da nuna ƙwazo wajen aikinsa.
Marigayin ya kasance tsohon wakilin gidan jarida na Triumph da RFI Hausa. Ya kasance wakilin gidan gwamnati na shekaru da dama.
Daga karshe yayi wa mamacin Addu’a, Allah ya jiƙansa, yayi masa rahama.
