Gwamnan Jihar Legas, Sanwo Olu yayi kira da mutane su kwantar da hankalin su a dalilin ruwan sama da aka samu kamar da bakin ƙwarya. Kwamishinan ruwa na Jihar shine yake faɗin haka a yayin wata sanarwa ranar Laraba.
Ruwan saman ya fara ne wajen karfe biyu na dare, sai dai mutane suka tashi suka ga ruwa ya cika masu ko ina har da ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar.
Wurare kamar su, Surulere, Ijesha, Okokomaiko, Ibeju-Lekki, Greenland Estate in Mende, Gbagada, Oshodi, Isolo, Lekki, Ikoyi, Ogba, Ikeja, da Ajah duk abun ya shafesu.
Har wasu tituna suma abun ya shafesu, don haka tafiya tayi wuya a cikinsu. Legas ta samu ruwan sama na awa tara ba tsayawa.
Amma Kwamishinan ruwa yayi kira da mutane su kwantar da hankalin su, gwamnati zatai iya bakin kokarinta domin shawo kan lamarin.
