Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
A ƙoƙarinsa na ganin Musulmi sun gudanar da bukukuwan Mauludi cikin farin ciki, jigon jam’iyyar APC na jihar Zamfara Hon. Yazid Shehu ɗanfulani ya ƙaddamar da rabon kayan abinci domin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).
An gudanar da rabon kayayyakin ne a shiyyar Zamfara ta tsakiya wanda ya ƙunshi Gusau, Maru, Tsafe da Bungudu.
A cewarsa, kayayyakin sun haɗa da buhunan shinkafa 140 da kuma katon ruwa da shaye-shaye 1,400 ga mabiya ɗariƙar Tijjaniyya a fadin kananan hukumomin huɗu.
Haka nan kuma mu ma an yi ta a lokacin Idi, domin an raba rago 109 ga malaman addinin Musulunci da sarakunan gargajiya a faɗin ƙananan hukumomin 4,” ya ƙara da cewa.
Hon. ɗanfulani, ya bayyana watan Mauludi a matsayin watan falala ga kowane Musulmi domin shi ne watan shedar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
A cewarsa, an yi hakan ne domin baiwa waɗanda suka ci gajiyar damar gudanar da Mauludi cikin sauƙi da jin daɗi.
Ya kuma shawarci al’ummar Musulmi da su yi amfani da watan Mauludi tare da addu’ar Allah ya dawo mana da zaman lafiya a jihar.
Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni a jihar da su taimaka wa marasa galihu musamman a halin da ake ciki na zamantakewar al’umma domin rage musu wahalhalu.
“Ina kira ga jama’a da su yi wa daidaikun jama’a a jihar nan da su riƙa amfani da abin da suke da shi wajen taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi a yankunansu musamman wannan halin da ake ciki da nufin rage wahalhalun zamantakewar al’umma a tsakaninsu,” ya ce.
