Mbappe na tantamar rattaɓa hannu a yarjejeniyarsa da Madrid

Kylian Mbappe zai zama ɗan wasan Real Madrid a kakar wasa mai zuwa, amma sai dai idan ba a samu sauyin yanayi ba, abu ne mai matuƙar wuya hakan. Sai dai har yanzu ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint-Germain tana fatan riƙe ɗan wasan na Faransa wanda ya ƙi saka hannu kan sabon kwantaragi kan ‘Los Merengues’.

Kylian Mbappe da Real Madrid za su haɗu a kakar wasa mai zuwa. Komai yana nuna cewa tauraron ɗan wasan zai isa Bernabeu a matsayin kyauta. Sai dai har yanzu PSG na da kwarin gwiwar cewa za ta iya shawo kan Mbappe.

A cewar Gianluca Di Marzio, idan Mbappe ya koma Real Madrid, zai samu Yuro miliyan 100 a kyauta. Kwantiragin ɗan wasan na Faransa zai kasance na tsawon shekaru biyar akan Yuro miliyan 50 a duk kakar wasa.

Duk da haka, akwai wani fitaccen batu da zai iya damun kulob ɗin.

Ɗan jaridar ya bayyana cewa, “sha’awar Kylian Mbappe ya yi yawa sosai har mahukuntan ƙungiyar Real Madrid sun yi ƙoƙarin aiwatar da yarjejeniya kamar wadda aka ƙulla da Cristiano Ronaldo a shekara ta 2008, amma Bafaranshen ba ya son sanya hannu kan komai.”

Ko da ya ke har yanzu kulob ɗin na Spain yana da ƙwarin gwiwa cewa yarjejeniyar baki da suka yi da wanda ya lashe kofin duniya zai zama gaskiya.