Kamfanin gandun dajin Sin zai dasa bishiyoyi Hekta 40,000 a duk ƙasar

Daga CMG HAUSA

Kamfanin kula da gandun daji na ƙasar Sin ya sanar cewa, zai shuka itatuwa da za su kai girman hekta 40,267 a faɗin ƙasar a wannan shekara ta 2022.

A cewar kamfanin, zai gudanar da aikin dashen itatuwa mafi girma da sauran ayyukan dake shafar kula da itatuwa bisa dacewa da yanayin yankunan ƙasar.

A matsayinsa na wani babban kamfani mallakin gwamnatin ƙasar a fannin kula da gandun daji, kamfanin kula da gandun dajin, ya samu ribar da ta kai RMB yuan biliyan 1.28, kwatankwacin dala miliyan 200 a shekarar 2020, wanda ya karu da kashi 64.7 idan an kwatanta da shekarar da ta gabata.

Ƙasar Sin ta shuka itatuwa kimanin hekta miliyan 3.6, da mai da girman hekta 380,800 na gonaki su zama filayen itatuwa a shekarar 2021, don tabbatar da ingancin muhallin ƙasar. Kuma ana daukar karin matakai don inganta gandun dajin, sannan an farfaɗo da wasu gandun dajin da suka kai girman hekta 933,300 a shekarar da ta gabata.

Fassarawa: Ahmad