Har yanzu ana keta ƙa’idojin da ƙasashen Asiya da Afirka suka gabatar

Daga CMG HAUSA

A ranar 18 ga watan Afrilun shekarar 1955, tawagogin gwamnatocin wasu ƙasashen dake nahiyoyin Asiya da Afirka 29, da suka haɗa da Afghanistan, da Sin, da Masar, da Habasha, da Laberiya, da India, da dai sauransu, sun gudanar da wani taro na musamman, a Bandung na ƙasar Indonesia, domin tattauna batun haɗin gwiwarsu, da na yaƙi da manyan ƙasashe masu mulkin danniya, inda suka gabatar da wasu ƙa’idoji guda 10, waɗanda ya kamata dukkan ƙasashe su yi ƙoƙarin binsu, don tabbatar da samun zaman lafiya a duniya, da ƙarfafa hadin kai tsakanin ƙasashe daban daban. Sai dai har ya zuwa yanzu, kimanin shekaru 67 ke nan da suka shuɗe, amma wata babbar kasa na ci gaba da keta wadannan ƙa’idoji guda 10, duk da cewa suna da matuƙar daraja a idanun jama’ar ƙasashen Asiya da Afirka.

Ƙa’idojin da ƙasashen Asiya da Afirka suka gabatar a Bandung sun hada da buƙatar girmama ikon mulkin kai, da zaman daidaito a tsakanin ƙasashe daban daban, da rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran ƙasashe. Sai dai, wata babbar ƙasa, ta kan kaddamar da yake-yake a duniya, da danne ƙananan ƙasashe, ta hanyar fakewa da sunan “yayata tsarin Dimokuraɗiya” da “ yaki da ta’addanci”. Kana ƙasar tana haddasa rikicin siyasa a ƙasashen dake nahiyoyin Turai da Asiya daban daban, inda take neman hamɓarar da gwamnatocin waɗannan ƙasashen, domin tabbatar da moriyar ƙashin kanta.

Ban da wannan kuma, ƙa’idojin 10 da aka gabatar, sun bukaci a magance ɗaukar matakan tsaro na haɗin kai, don kare moriyar wata babbar ƙasa. Har ila yau, an ce kada wata ƙasa ta matsawa sauran ƙasashe lamba. Sai dai wannan babbar ƙasa har kullum tana ƙoƙarin neman kafa wasu rukunai a duniya, inda ake shata layi tsakanin ƙasashe bisa tsarin siyasa, da tilasta sauran ƙasashe zabar wani ɓangare, lamarin da ke haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin ƙasashen duniya.

Har ila yau, ƙa’idojin 10 da ƙasashen Asiya da Afirka suka gabatar sun buƙaci a ƙarfafa haɗin kai a tsakanin ƙasashen don tabbatar da moriyarsu ta bai ɗaya, da wanzuwar adalci a duniya. Sai dai a nata ɓangaren, wata babbar ƙasa tana kallon moriyar kanta a gaban ta sauran ƙasashe. Inda ba ta lura da tsarin ciniki da ya shafi ɓangarori daban daban ba, kana tana tsammanin dokar cikin gidanta ta fi dokokin ƙasa da kasa muhimmanci. Ƙasar na ta ƙoƙarin ƙaƙaɓa wa sauran ƙasashe takunkumi, da dasa wa kamfanonin sauran ƙasashe shingaye, da mallake kaddarorin sauran ƙasashe yadda ta ga dama.

Sa’an nan ƙa’idojin 10 da aka gabatar sun buƙaci a daidaita sabani ta hanyar yin shawarwari da sulhuntawa. Amma wannan babbar ƙasa, idan ta ga ƙasashen dake yaki da juna sun zauna a gaban teburin shawarwari, to, nan take za ta fara ƙulle-ƙullen makirci tare da samar wa ɓangarorinsu makamai, saboda bata son ganin bayan yake-yake. Tana fatan ganin yaƙi ya ɗore sosai, ta yadda kamfanoninta dake ƙera makamai sun samu ƙazamar riba, yayin da ita ma za ta samu damammaki na dakile cigaban sauran ƙasashen da suke gogayya da ita.

Ba sai na ambaci sunan wannan babbar ƙasa ba, domin kowa ya san ta. Sai dai duk irin girman tasirin da wata babbar ƙasa ke tinkaho da shi, wata rana tasirinta a duniya zai zo ƙarshe, dama da komai nisan jefa wata rana ƙasa zata faɗo inji ‘yan magana. Matuƙar dai ƙasashen dake nahiyoyin Asiya da Afirka, da sauran yankunan duniya, za su tsaya tsayin daka don tabbatar da haɗin kai, da nuna adawa ga mulkin danniya, to ba shakka, akasarin ƙasashe masu adalci za su ci nasara a ƙarshe.

A wannan lokacin da muke cikin watan Ramadan mai tsarki, bari mu yi addu’a ga Allah, don ya kawo ƙarshen mulkin danniya a duniya, da samar mana da zaman lafiya mai ɗorewa. Amin.

Fassarawa: Bello Wang