Me ya hana Hon. Goro halartar bikin shekaru 25 da ƙirƙiro Ƙaramar Hukumar Fagge?

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

A cikin makon jiya ne Ƙaramar Hukumar Fagge ƙarƙashin jagorancin Hon. Ibrahim Shehi ta gudanar da taron bikin cika shekaru 25 da ƙirƙiro ƙaramar hukumar.

Sai dai rashin halartar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Fagge, Honorabul Aminu Suleiman Goro taron ta sa ake ganin tamkar bai ɗauki al’amarin da muhimmanci ba, duk kuwa da cewa yana daga cikin waɗanda suka fi cin moriyar albarkacin zaman ƙaramar hukumar Fagge.

Wasu na ganin wannan tsantsar nuna rashin karramawa ce ga al’ummar da xan majalisar tarayya na Faggen ya yi ga taron, domin ba na siyasa b ane, taro ne na dukkan al’ummar Fagge da aka gayyaci kowa har ma da waxanda ba ‘yan yankin ba sun halarta.

Wata majiya ta ce ko a ranar da aka gudanar da taron shi ɗan majalisar ya je Unguwar Sabongari halartar taron karramawa da aka yi masa.

Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar musamman dattawa da malaman addini da na zamani da tsofaffin shugabannin ƙaramar hukumar da tsoffin ‘yan majalisu, da ɗan majalisar jiha mai ci dabke wakiltar yankin daga jam’iyyar PDP, Honorabul Tukur Muhammad wanda ya turo wakili kasancewar ba ya gari a yayin taron. 

A yayin taron da aka gudanar a harabar Sakatariyar mulki ta Fagge, an gudanar da jawabai da kuma jinjina wa Marigayi Shugaban Ƙasa Sani Abacha wanda a lokacin mulkinsa ne ya ƙirƙiro ƙarin ƙananan hukumomi a ƙasar nan har da Fagge.

An kuma karrama mutane da dama da suka bada gudunmuwa a fannoni daban-daban ga ci gaban yankin, ciki har da tsohon Kakakin majalisar dokokin jihar Kano Honorabul Yusuf Abdullahi Atah.