Yadda haƙuri da juriya suka kai Dr. Jibril Lawal Tafida ga matakin nasara

Daga BABANGIDA KAKAKI 

In ka ji wane ba banza ba, in ba a sha dare ba, an sha rana. Wannan magana haka take, musamman idan aka yi duba a cikin ayyukan wasu mutane waɗanda suka ɗauri aniyar kafa tarihi da taimaka wa al’umma don samun ci gaba.

A ran 18 ga watan Nuwamban 2021 ne, Jami’ar Gwamnatin Tarayya, wato Federal University Lokoja, ta jihar Kogi ta bayar da digirin girmamawa ga Alhaji jibril Lawal Tafida, wani hamshaƙin ɗan kasuwa, kuma mai taimakon al’umma, sannan ɗan siyasa mai aƙida da ƙoƙarin ganin an kamanta gaskiya da adalci, ɗan asalin jihar Kaduna.

Jami’ar ta ba shi digirin girmamawa ne a wajen bikin yaye ɗalibanta karo na biyar. Bikin da ya samu halartar manyan mutane da ƙanana daga dukkan faɗin ƙasar nan.

Daga cikinsu akwai tsohon gwamnan jihar Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Dokta Muktar Ramalan Yero da ‘yan tawagarsa, wasu manyan jihar Kaduna. 

Dokta Jibril Tafida mutum ne wanda ke zaune da kowa lafiya, babba da ƙarami. Mutum ne mai wayau da hangen nesa da kuma hikima.

Ga duk wanda ya san shi ba zai yi mamakin wannan girmamawar da Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta ba shi ba.

Dr. Tafida ɗan shekaru kusan hamsin ne, ɗan kasuwa ne, kuma ɗan siyasa ne wanda ya ratso hanyoyi masu ƙaya da tsaido har yake cimma nasarorin al’amurran da ya sanya a gaba. Kuma hakan ne ya ɗaga darajarsa da martabarsa har duniya ta san shi. Ya yi takarar siyasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sau da yawa yana neman kujerar ɗan majalisar tarayya daga mazaɓar Kaduna ta Kudu.

Dokta Tafida mutum ne wanda yake alamta nasarori a harkokin siyasa da kasuwanci da kuma taimakon bayin Allah, abubuwan da suka mayar da shi abin koyo, kuma Allah sam-barka a wurin jama’a. Amma kada a shafa’a, shi mutum ne mai sauƙin hali, wanda babu abinda ke ba shi tsoro ko tunzura shi ya aikata ba daidai ba.

Ta wace hanya ya cimma waɗannan ɗabi’un? Sirrinsa kamar yadda bincike ya nuna shi ne ya fahimci caccanzawa da jujjuyawar al’amurran rayuwa cikin hikima da dabaru. Na farko dai, ya yi nazarin ɗabi’ar rayuwa wadda gwagwarmaya ce tsakanin ƙarya da gaskiya. Don haka, ya zaɓi ya yi abinda ya dace da kuma bayar da gudunmuwarsa don ya yi kirki da gaskiya wajen ƙoƙarin yin galaba akan rashin ƙarya.

Tabbas, Dokta Tafida ya zavi ba wai kawai ya aikata alheri ba ne, har ma ya kafa tarihin da ba za a manta da shi ba. Abu na biyu, shi ne sai ya samu cikakken ilimi da gogewa a aikace domin ilimi shi ne gishirin zaman duniya. Bai yi wasa da neman shi ba ko kaɗan. Har yanzu cikin neman ilimi yake.

Sirri na uku shi ne ƙulla dangantaka da aiki tare da mutane daban-daban daga dukkan faɗin ƙasar nan. Shi mutum ne mai tausayi da girmama ‘yan adam, farko dai danginsa sai abokansa da abokan huɗɗoɗinsa imma a harkar kasuwanci ko siyasa ko wasu mu’amalolin rayuwa ba tare da la’akari da bambancin addini ko aƙida ko ƙabila ko inda mutum ya fito ba. 

Daga nan, sai ya rungume sirrin bai wa da taimakawa al’umma, wadda ta wannan hanyar ne ya samu ɗaukaka da yin fice a bainar jama’a.

A harkar kasuwanci kuwa, wadda akan ta ne ya samu girmamawa mafi girma da ɗaukaka a halin yanzu, Dokta Tafida ya ba maraɗa-kunya, domin ya fuskanci ƙalubale da jarabawoyi inda ya jajurce ya yi galaba akansu ɗaya bayan ɗaya.

A cikin shekaru sama sa ashirin, ya kafa Rukunin Kamfanonin JITA, wanda ya yi fice a harkar aikin gona, kiwon kajin turawa da na gida da kiwon kifi da noman amfanin gona irinsu masara da waken soya, sannan daga baya ya tsunduma a harkar filaye da gina rukunin gidajen kwana da shagunan kasuwanci wato ‘Shopping Malls’ a jihar Kaduna da Babban Birnin tarayya Abuja da sauran jihohin Arewacin ƙasar nan. 

Shigarsa a harkar zirga-zirga wata hanya ce wadda ya shiga a cikinta wadda ta samar wa mutane ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin jihar Kaduna da ƙasar nan. Don haka, a ƙarƙashin Rukunin Kamfanonin JITA, Dokta Tafida yana da manyan kamfanoni guda uku masu rassa daban-daban waɗanda ke jujjuya biliyoyin nairori da samar da ayyukan yi ga dubban mutane da samar da amfani ga al’umma ta fanni daban-daban.

Watakil mai karatu zai so ya yi tambayar cewa, wane darasi mai kyau al’umma za su koya daga wannan digirin girmamawar?

Girmamawa ce ga Dokta Tafida wanda ya jajurce wajen yin namijin ƙoƙarinsa ya tabbatar da cancantarsa wadda ta yi galaba akan ƙalubalen da ke tattare da harkar kasuwanci da kuma ƙoƙarinsa da hikimarsa ta ririta dukiya.

Idan aka yaba wa mutanen dake yin abin kirki, hakan na ƙara basu ƙarfin guiwa su ci gaba, ta yadda har wasu mutanen ka iya kwaikwayonsu. Haka ɗabi’ar take. 

A ɗayan vangaren kuma, wannan digirin abin yabo ne ya dace al’ummar qasar nan ya kamata ta nuna jin daɗinta da kuma kwaikwayo musamman ‘yan kasuwar da suke da niyyar faɗawa fagen kasuwancinsu amma tsoron yanayin yana hana su fuskantar ƙalubale. Sai abu na uku, wannan digirin yabo nasarar gaskiya ce akan ƙarya, adalci akan akasinsa, ƙoƙari akan kasala da sauransu.

Dokta Tafida mutum ne mai ƙololuwar tausayi ga kowane irin mutum. Alherinsa kamar ya so ya yi waya, kuma yana yi ne don Allah. Shi mutum ne wanda tunane-tunanensa da ayyukansa yana yi ne domin kafa tarihi da kuma jin daɗin al’ummarsa.

Akan haka ne, masu nazarin ɗabi’un al’umma suka haƙiƙance cewa, waɗannan ɗabi’un ne suka kai shi matsayin da ya ke a rayuwarsa.

A tarihance, Dokta Tafida an haife shi kuma ya girma a garin Kaduna a farko shekarun 1970. Bayan kammala makarantar firamare da sakandarensa, ya yi karatun difiloma a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna watk  Kaduna Polytechnic. 

Ya ɗan yi aiki da jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo kafin ya bari ya tsunduma siyasa da kuma harkokin kasuwanci. Shi mutum ne wanda ya shahara a fanni aƙalla uku: Siyasa da kasuwanci da kuma taimakon al’umma marassa galihu da marayu da talakkawa.

A siyasa, shi ɗan takara ne ko a gobe na ɗan majalisar dokoki ta tarayya, kuma al’umma na jiran a kaɗa gangar siyasa su zaɓe shi. A fagen kasuwanci, rukunin kamfanoninsa na JITA sanannun kamfanoni a harkar kiwon kajin turawa da na Hausa da noma da harkar gina gidaje da filaye a jihar Kaduna da Abuja da wasu jihohin ƙasar nan. Sannan ga motocin gaya na sufuri waɗanda ke ɗaukar fasinjoji da kaya zuwa garuruwan faɗin ƙasar nan. 

A ƙarshe, wannan digirin girmamawa a fannin tattalin arziki, babban abin yabo ne ga Dokta Tafida da kuma tabbacin cewa, yabon gwani ya zama dole, kuma har gobe ruwa na maganin dauɗa.

Kakaki ɗan jarida ne, kuma Shugaban kamfanin mujallar turanci ta BALLPOINT da ke Kaduna.