Tabbas za mu miƙa mulki ga waɗanda suka ci zaɓe a 2023 – cewar Buhari

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bai wa ‘yan Nijeriya da sauran ƙasashen duniya tabbacin gudanar da sahihin zaɓe ya zuwa 2023 tare da miƙa ragamar mulki cikin lumana.

Mai magana da yawun Buhari, Mr Femi Adesina ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja a Juma’ar da ta gabata. Yana mai cewa, Buhari ya bada tabbacin nasa ne yayin wani babban taro da shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden ya shirya ta bidiyo kan harkar dimukuraɗiyya.

Buhari ya ce za a tanadi dukkan abubuwan da ake buƙata domin tabbatar da Nijeriya ta sake shaida miƙa mulki cikin kwanciyar hankali.

Ya ce, “Yayin da lokacin babban zaɓen 2023 ya ƙarato, mun maida hankali wajen tanadar da dukkan abubuwan da ake buƙata don tabbatar da Nijeriya ta shaida sahihin zaɓe da kuma miƙa mulki cikin aminci da salama.”

Buhari ya shaida wa taron cewa Nijeriya za ta ci gaba da mara wa sha’anin dimukuraɗiyya baya a yankin Afirka ta yamma da ma sauran yankunan Afirka.

Buhari ya nuna takaicinsa dangane da yadda a lokutan baya ake ƙwace mulki da ƙarfin tsiya a wasu ƙasashen Afirka.

Yana mai cewa, ya zama wajibi ƙasashen duniya su ƙyamaci yadda wasu shugabanni kan yi wa kundin tsarin mulkin ƙasashensu kwaskwarima don su yi daidai da muradunsu, lamarin da ya ce ya zama tilas a daƙile ci gaba da faruwan hakan.

“Lallai Nijeriya ta bada cikakken goyon baya ga ECOWAS don magance ƙalubalen da ake fuskanta, ta kuma yaba da goyon bayan da Ƙungiyar Haɗa Kan Afirka da Majalisar Ɗinkin Duniya suka bayar”, in ji Buhari.

A cewar shugaban, Nijeriya na ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro wanda hakan ke yi wa dimukuraɗɗiyar ƙasar babbar barazana.

Daga nan, Buhari ya yi kira ga ƙasashen duniya da su taimaka su mara wa Nijeriya baya wajen daƙile ‘yan ta’adda da harkokinsu a faɗin ƙasar.