Sama da mutum 400 aka kashe a Nijeriya cikin watan Nuwamba – Bincike

Daga SANI AHMAD GIWA

Wani rahoto da kamfanin Beacon Consulting da ke fitar da rahoto tare da bayar da shawarwari ga mahukunta game da matsalar tsaro a Nijeriya duk wata, ya wallafa rahoton sa na watan Nuwamba, inda ya ce an kashe sama da mutane 400 a watan, sannan satar jama’a ta ƙaru yawanci a arewacin ƙasar.

Rahoton ya kuma ce an yi kisan ne a jihohi 28 na Nijeriyar a ƙananan hukumomi 115 a cikin watan Nuwamba kaɗai.

A cewar rahoton, satar mutane a Nijeriya ta ƙaru da kusan kashi 38 cikin ɗari a Nuwamba idan aka kwatanta da alƙalumman rahoton na watan Oktoba. Alƙalumman sun nuna mutum 363 aka sace a sassan Nijeriya a watan Nuwamba.

Rahoton ya kuma ce an samu raguwar yawan mutanen da aka kashe da kimanin kashi 41 a ƙasar idan aka kwatanta da rahoton watan Oktoba da kamfanin ya ce an kashe mutum 636.

Rahoton watan Oktoba ya nuna wata huɗu a jere ana kashe sama da mutum 600 a Nijeriya tun a Yuni, watan da aka fi kashe mutane a Nijeriya a 2021 inda aka kashe mutum 1031.

Rahoton ya nuna yadda kamfanin ya gudanar da nazari da bincike da tattara alƙalumansu a watan Nuwamba. Da kuma girman barazanar kai hare-hare a arewacin Nijeriya duk da matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka da jihohi.

A cewar rahoton alƙaluman sun haɗa da yawan mutanen da aka kashe sakamakon rikicin Boko Haram, da kuma na ‘an fashin daji a arewa maso yammaci da tsakiyar Nijeriya da ma waɗanda jami’an tsaro suka kashe a bakin aiki, da kuma su kansu jami’an tsaro da suka rasa rayukansu a fagen daga.

Akwai kuma ƙaruwar laifuka a yankin kudu maso yammacin Nijeriya da yanayin zave a jihar Anambara da fasa gidan yari da aka yi a jihar Filato.

Rahoton ya nuna yadda aka dawo da hare-haren ‘yan bindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa a hanyar Abuja zuwa Kaduna. Akwai kuma ƙaruwar rikicin da ya shafi na siyasa.

Rahoton ya nuna cewa yankin Arewa maso yammaci aka fi kashewa da satar mutane fiye da sauran sassan Nijeriya.

Alƙalumman rahoton sun nuna cewa an sace mutum 204 tare da kashe mutum 163 a watan Nuwamba. Alƙalumman sun nuna an samu raguwar yawan mutanen da aka kashe a yankin a watan Nuwamba idan aka kwatanta da rahoton Oktoba inda aka kashe mutum 258 a Arewa maso yammaci.

A arewa maso tsakiya mutum 133 aka sace a cewar rahoton, yayin da aka kashe 37 a yankin.

A Arewa maso gabashi, rahoton ya ce mutum biyar aka sace yayin da aka kashe mutum 151 a watan Nuwamba.

Rahoton har wa yau, ya ce bincikensa ya sa ido kan ayyukan jami’an tsaro kan yaƙar ‘yan bindiga a arewa maso tsakiya da Arewa maso yammaci a watan Nuwamba, kuma an kashe ‘yan bindiga tare da cafke da dama.

Sai dai a cewar rahoton farmakin jami’an tsaron ya kasa hana kai hare-haren ‘yan bindiga kan al’umma musamman yunƙurin ‘yan bindigar da kwace iko a yankunan Neja da Sakkwato da Zamfara da tursasa wa manoma biyan haraji ƙarƙashin jagorancin shugaban ‘yan bindigar da ake kira Bello Turji.

Rahoton ya ce ana ci gaba gaba da gwabzawa tsakanin jami’an tsaron Nijeriya da mayaƙan Boko Haram da na ISWAP a yankin Arewa maso gabashi. A cewar rahoton, hare-hare ta sama ya karya lagon mayaƙan Boko Haram da ISWAP wajen rage masu ƙarfin kai hare-hare a yankin Borno da Yobe da Adamawa.

Amma ISWAP da Boko Haram na ci gaba da zama barazana inda suke ƙoƙarin ƙwace ikon garuruwa da kuma kai hari da tare mutane musamman a yankin Borno, a cewar rahoton.

Rahoton na ƙwararru ya ce akwai buƙatar a yi shirin ko ta kwana musamman kan nasarorin da jami’an tsaro ke samu wanda zai iya haifar da hare-hare na ramuwar gayya daga ‘yan bindiga a yankin arewa maso tsakiya da arewa maso yammaci.

Binciken ya yi barazanar cewa hare-haren da satar mutane za su ƙaru saboda halin matsi na tattalin arziki da ake ciki a Nijeriya da kuma tsadar farashin kayyaki a ƙasar.

Rahoton ya yi kira ga hukumomin ƙasar su fara yin ƙoƙarin magance rashin yardar da ta yi katutu a tsakanin ‘yan ƙasar da nufin daƙile yawan kashe-kashen mutane da ake fama da shi.

An kuma buƙaci hukumomi su ɓullo da matakan inganta tsarin zamantakewar da ya taɓarɓare musamman a arewacin Nijeriya da kuma tabbatar da hukunci ga masu aikata laifuka a ƙasar.