Mun rasa fiye da mutum 1000 a kisan kiyashin Zariya – ‘Yan Shi’a

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Harkar Musulunci a Nijeriya ta sake yin kira da a tabbatar da adalci ga ɗaruruwan ‘ya’yanta da ake zargin sojojin Nijeriya sun kashe a watan Disambar 2015 bayan wani farmaki da sojojin suka kai bisa zargin tare wa shugaban hafsan sojin ƙasa na lokacin, Laftanar Janar Tukur Buratai hanya a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.

A wata sanarwa da harkar ta fitar a ranar Juma’a mai taken ‘Kira da Adalci ga waɗanda aka kashe a Zariya’, harkar ta bayyana cewa, waɗanda lamarin ya rutsa da su sun kai mutum 1,000 na kowane jinsi da shekaru da sojoji suka yi wa jana’izar jam’i da daddare a asirce babu wanda ya sani.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Farfesa I.M. Mshelgaru na ƙungiyar ‘Academic Forum’ ta harkar, ta kuma bayyana cewa, an kashe yara 193 da mata masu juna biyu 23, yayin da aka share iyalai na kusan gidaje 23 gaba ɗaya a doron ƙasa.

Harkar ta yi Allah wadai da hujjar da ake zargin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar na cewar, “ba wani abu bane na damuwa, illa wasu ƙananan yara ne kawai suka bugi ƙirjin wani Janar,” a yayin wani taron manema labarai.

Harkar ta ce, saɓanin kisan kiyashin da sojoji suka yi wa masu zanga-zangar #EndSARS a ranar 20 ga Oktoba, 2020 a Lekki, wanda Gwamnatin Tarayya ta yi duk mai yiwuwa wajen musanta haka, babu wata hujja ko takamammen shaida ta musanta kisan kiyashin Zariya.

Ta koka da cewa, duk da sakamakon da kwamitin bincike na shari’a da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa na cewa sojoji sun kashe ‘yan Shi’a 347 tare da yi musu jana’iza a asirce, amma har yanzu ba a kama waɗanda suka aikata laifin ba tare da hukunta su.

Harkar ta ce, tana ganin ya dace ta dawo da buƙatarta na neman adalci ko da shekaru shida bayan ‘pogrom’ tare da buga talla domin ya zo daidai da ranar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

Harkar ta ƙara da cewa, “a bayanan mu, sama da mutane 1,000 da suka je Zariya a wannan baƙar rana, waɗanda da yawansu aka gansu a wurare daban-daban wajen kisan kiyashin, ba su koma gidajensu ba.”

Harkar ta ci gaba da cewa, “saboda haka, kuma abin baƙin ciki, iyalai da yawa sun rasa aƙalla mutum ɗaya zuwa uku yayin da wasu iyalai suka ƙare gaba ɗaya. A gaskiya, muna so mu sake ambata kaɗan daga cikin waɗanda aka kashe kuma an san su aƙalla a cikin al’ummomin da suke rayuwa, wato kamar, ’yayan Shaikh Zakzaky guda uku – Hammad Ibraheem, Ali Ibraheem da Humaid Ibraheem – an kashe su a gaban iyayensu.”

“An kashe Dakta Mustapha Sa’id, likitan Sheikh Zakzaky tare da ’ya’yansa maza uku – Muhammad Mustapha, Ali Mustapha da Ruhullah Mustapha. ’Ya’yan Injiniya Yahaya Gilima da ke Kaduna su uku sun yi shahada a lokacin kisan kiyashin. Sai Buhari Jega wanda ya yi karatun digirin-digirgir (PhD) a fannin kimiyyar siyasa kuma malami na wucin gadi a jami’ar Abuja. An kashe Buhari da matarsa, A’isha, ‘yarsu ‘yar watanni 16, Batool, da kuma wasu ƙannen matarsa ​​guda biyu a lokacin kisan kiyashin.”

“Haka kuma an kashe ‘ya’yan Dakta Isah Gwantu guda huɗu, malami a Sashen Sadarwa na Jama’ar ABU, kuma Mawallafin Jaridar Education Monitor. Yaransa su ne Muhammad Waziri da Fatima Waziri da Hassan Waziri da Hussaini Waziri. Ba wai kawai aka kashe Malam Abudllahi Abass Zaria ba amma ‘ya’yansa shida – Abdurrazaq, Abbas, Muhammad, Ahmad, Ibrahim da Jawad – duk sojojin Nijeriya ne suka kashe su,” inji harkar.

Ta ce, “waɗannan kaɗan daga cikin waɗand aka kashe, ban da ɗimbin adadin waɗanda suka jikkata a matakai daban-daban, ko dai daga harbin bindiga ko ƙona.”

Harkar ta yi kira da a hukunta duk waɗanda suka taka rawa ko ɗaya wajen kisan gilla da kuma abin da ya biyo baya.

Ta kuma buƙaci a gaggauta sakin waɗanda (’yan harkar) da ke tsare ba tare da wani sharaɗi ba, da kuma a ba su fasfo ɗin Sheikh Zakzaky da mai ɗakinsa Malama Zeenat domin a ci gaba da duba lafiyarsu a kowane ƙasar da suke so inda ƙwarewar da ake buƙata.