Minista ya buƙaci masu harkar ma’adanai su zauna lafiya

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Ministan ma’aikatar bunƙasar harkokin ma’adanai, Dele Alake ya yi kira na musamman ga duka hukumomi masu harkokin haƙa da sarrafa ma’adanai musamman a ƙaramar Hukumar Nasarawa da jihar Nasarawa baki ɗaya su zauna lafiya da juna a yayin da suke gudanar da harkokin nasu.

Ministan Dele Alake ya yi kiran ne jim kaɗan bayan wani zama na musamman da ya yi da gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule da wasu muƙarraban gwamnatinsa a gidan gwamnati dake birnin Lafiya fadar jihar ranar Litinin na mako da ake ciki.

Dele Alake wanda darakta janar ɗinsa a wani shashin ma’aikatar da ake kira Cadastry a Turance ya wakilce shi ya ce ba shakka kiran ya zame wajibi idan aka yi la’akari da muhimmancin zaman lafiyar tsakanin masu harkokin ma’adanan don ta haka ne kawai za su samu ci gaba da bunƙasar harkokin nasu a duka matakai.

Ya ce dole ne a yanzu haka hukumomin daban-daban a jihar su haɗa kai su koma teburin sasantawa don warware duka rigirgimu dake tsakanin su kasancewar a cewarsa sai da zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu kaɗai hukumomi masu zuba jari daga gida Nijeriya da ƙasashen waje za su samu damar cigaba da zuba jarinsu a harkokin ma’adanan a ƙaramar hukumar ta Nasarawa da jihar bakiɗaya.

Ministan Dele Alake ya kuma yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da abin da ya bayyana a matsayin gagarumin gudumawa da gwamnatin sa ke bayar akai-akai wajen bunƙasar harkokin ma’adanan da safararsu a duka matakai inda ya ce tabbas hakan nema ya aza jihar a mataki na gaba-gaba a ƙasar nan a fannin cigaba da bunƙasar ma’adanan a yanzu haka.

Daga nan sai ministan ma’aikatar ta bunƙasar harkokin ma’adanai ta ƙasa Dele Alake ya kuma yi amfani da damar inda ya sanar cewa tuni ma’aikatarsa ta yanke shawarar gudanar da wani gagarumin taron ta wanda ana sa ran gudanar a watan Nuwambar shekarar 2024 da ake ciki kuma ma’aikatar tuni ta zabi jihar ta Nasarawa a matsayin wajen da za a gudanar da taron bayan ta yi la’akari da ire-iren gagarumin gudumawa da take bayar akai-akai wajen bunƙasar harkokin ma’adanan ta da ta ƙasa bakiɗaya.

A nasa ɓangaren da yake jawabi gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule bayan ya godewa bakin nasa dangane da ziyarar ta musamman da kuma zabin jihar tasa a matsayin inda za a gudanar da babban taron ma’adanan ya kuma tabbatar masa cewa a shirye gwamnatin sa take ta cigaba da bai wa fannin fifiko kasancewar Allah ya albarkaci jihar da dinbin ma’adanai iri daban-daban da sauransu.

Sauran manyan baƙi da suka yi jawabi a yayin ziyarar ministan ma’adanan zuwa jihar ciki har da kwamishinan ma’aikatar ma’adanai da albarkatun ƙasa na gwamnatin jihar Honorabul Kwanta Yakubu duk sun yi fatar alheri suka kuma yi alƙawarin cigaba da yin duka mai yuwa don tabbatar da ɗorewar nasarori da ake samu a fannin na harkokin ma’adanai a jihar kawo yanzu.   

By ukarofi