Ministan Abuja ya kira taron gaggawa kan matsalar tsaro

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Ministan Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya kira taron gaggawa a ranar Talata kan matsalar tsaron da ke addabar babban birnin kasa.

Ministan ya bayyana haka ne sa’ilin da yake jawabi a wajen wani taro a Abuja, inda ya bai wa mazauna yankin tabbacin ba su kariya yadda ya kamata.

Ya kara da cewa gwamnati na yin mai yiwuwa wajen karfafa wa hukumomin tsaro ta hanyar samar musu da dukkan abubuwan da suke bukata don dakile matsalar tsaro a fadin birnin.

MANHAJA ta kalato cewa, wadan suka halarci taron gaggawar sun hada da shugabannin hukumomin tsaro na FCT, manyan jami’ai na hukumar gudanarwar Abuja, shugabannin yankunan hukumomin Abuja da kuma sarakunan gargaji na yankin.

Wike ya gargadi shugannin hukumomin yankin da kowa ya yi tsayin daka wajen sauke nauyin da ke kansa yadda ya kamata.

A lokutan baya-bayan nan daian fuskanci matsalolin tsaro a wasu sassan birnin Abuja inda aka fi wasu har gida aka yi garkuwa da su.

By Editor