Tate da ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A ƙarshe dai tsohuwar Ministar Ma’aikatar Jinkai da Yaki da Talauci Betta Edu ta yi gaba, sai dai tashin zance. Amma ’yan Nijeriya za su dade ba su manta da ita ba a matsayinta na minista mai gajeren kwana, wacce cikin kankanin lokaci son zuciya da rashin gaskiya suka yi awun gaba da kujerarta.
Dama a cikin jawabinsa na sabuwar shekara, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatarwa da ’yan Nijeriya cewa kamar yadda ya dauki rantsuwar kama aiki na yin dukkan abin da ya kamata don inganta cigaban kasar nan. Shi da ministocinsa da masu rike da muqaman gwamnati ba su da wani sauran uzuri wa ’yan Nijeriya na rashin yin abin da ya kamata. Don haka kowanne minista ya shafawa kansa ruwa, kar ya bari a same shi da rashin gaskiya.
Za a iya cewa wannan abu da ya samu tsohuwar minista Betta Edu, da takwararta ta lokacin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sadiya Umar Farouk, da tsohuwar shugabar Hukumar Kula da Walwalar Jama’a Halima Shehu, da ministan kula da harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo, tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro. Abubuwa da yawa suna faruwa na rashin gaskiya da almundahana a ma’aikatu daban-daban wanda idan ba bincike ne ya biyo ta kansu ba ba a sani, sai bayan tsawon lokaci. Babu ma kamar irin waxannan ma’aikatu da hukumomi da ake bai wa maqudan kudade da za a yi amfani da su don kyautata rayuwar talaka. An fi yin aringizo da sama da fadi, saboda yaudarar da ake yi wa jama’a da sunan ana ba da tallafi.
Tun bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi, da yadda tsadar al’amura suka jefa rayuwar talaka cikin wani yanayi ya sa ala tilas gwamnati ta dauki matakan gaggawa na samar da tallafin kudade da kayan abinci ga mutanen da ke fuskar kunci da tagayyara. Sai dai abin takaici yadda aka rika mayar da abin ya zama siyasa, ana bai wa gwamnoni da ’yan majalisu makudan kudade don su rabawa jama’arsu, su kuma sai suka koma gyara siyasar su. Kowa sai yadda ya ga dama ko wadanda ya so su amfana kafin su samu.
Kwanan nan qungiyar Lauyoyi Musulmi ta MURIC ta kalubalanci ’yan Majalisar Kasa game da rabon kayan abinci da gwamnatin tarayya ta ba su kudade su yi a yankunansu, don rage radadin talauci, amma sun yi mirsisi a kan kudaden ba sa ma ko maganar su.
Wannan zargi ya fito ne bayan da wani dan majalisar wakilai daga Jihar Edo ya bayyana a wani bidiyo da aka yi ta yaɗawa, yana nuna wani katafaren rumbun adana kayan abinci da ya tanada domin rabawa talakawa a yankin mazabarsa. Abin da ya sa sauran ’yan qasa bincikar me sauran ‘yan majalisar suke yi da nasu kudaden da aka ba su, kodayake wasu a cikinsu ma sun karyata cewa kudaden ba su shiga asusunsu na banki ba.
Bincike ya nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta bai wa mambobin Majalisar Wakilai ta Tarayya su 360 Naira Miliyan 100 kowannensu, yayin da aka bai wa mambobin Majalisar Dattawa 109, zunzurutun kudi har Naira Miliyan 200, domin sayen kayan abinci da za a rabawa talakawa a madadin Gwamnatin Tarayya. Amma wadannan bayin Allah ba sa ma zancen su, ga shi lokaci sai tafiya yake yi, daga lokacin da gwamnatin tarayya ta ayyana fitar da wadannan kudade, bayan Naira Biliyan 20 da aka bai wa Gwamnoni.
A nan ya zama wajibi mu jinjinawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa himma da ƙoƙarin da yake yi na ganin ya daidaita tafiyar al’amura da saukakawa talaka don ya samu sassauci daga halin da tsare-tsaren gwamnati suka sanya shi a ciki. Abin mamaki ne a ce rijiya ta ba da ruwa, amma guga tana hanawa!
Ko shekara wannan gwamnati ba ta yi a kan mulki ba, amma ’yan siyasa da masu riqe da manyan mukaman gwamnati sun baza komarsu sai wawurar dukiyar da aka ware don jinkan jama’a suke yi. Tun ma kafin a gama fahimtar ina gwamnati ta dosa ko kuma yaya kamun ludayinta zai kasance.
Bayanan da ke fitowa daga hukumomin gwamnati daban-daban masu alaka da bincike kan zarge-zargen almundahanar kudaden da ake tuhumar tsohuwar minista Betta Edu da yin ba daidai ba a kansu na nuni da cewa, zargin ya fara bayyana ne sakamakon wani umarni da ministan ta bayar na cewa a tura wasu kudade da suka kai Naira Miliyan 585.189 zuwa ga wani asusun banki na kashin kai mallakar wata Bridget Mojisola Oniyelu wacce aka ce ita ce Mai Binciken Kudi taa shirin ba da tallafin kudade ga kungiyoyin gajiyayyu a Ma’aikatar Jinqai. Zargin da Kakakin Ma’aikatar Rasheed Zubair ya ce, babu wani abu da aka yi da ya savawa doka.
Sai dai za a iya cewa, allura ta tono garma. Domin kuwa an sake bankado cewa akwai wani bincike da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta gudanar wanda ya gano cewa, ita ma tsohuwar Ministar Ma’aikatar Jinqai ta zamanin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sadiya Umar Farouq, tana fuskantar tuhuma kan wasu makudan kudade har Naira Biliyan 32 da ake zargin sace su aka yi daga Ma’aikatar Jinkai a tsakanin watan Yuli zuwa Agusta na shekarar 2023.
Sannan bayan wannan zargin, ita ma Hukumar EFCC a nata bangaren bangaren tana tuhumar tsohuwar minista Sadiya Umar Farouq kan wasu kudaden Naira Biliyan 37 da ake zargin an yi rub-da-ciki a kansu ne.
Babu shakka wadannan zarge-zarge da ake yi wa Hukumar Kula da Jinkai da Walwalar ’Yan Kasa ko kuma kamar yadda yanzu aka canza mata suna zuwa Hukumar Yaqi da Talauci da Jinqan Al’umma tana samun kudade na fitar hankali tun daga tsohuwar gwamnati zuwa yanzu, wadanda ake fitarwa don tausayawa jama’a masu fama da talauci da wadanda yake-yake da ta’addanci suka tagayyara, amma abin mamaki sai gashi saboda rashin tausayi da imani, wasu tsiraru ne suke warwaso da kudaden, suna arzuta kansu.
An gano cewa, a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024 wannan ma’aikata ta jinkai ta samun zunzurutun kudaden da yawansu ya haura Naira Tiriliyan 2 da Biliyan 38, bisa kididdigar da ofishin kula da tsare-tsaren kasafin kudi ya fitar.
A gaskiya wadannan zarge-zargen da suke fitowa ba su kamata a ce an samu da jami’an gwamnatin da ko shekara daya ba ta cika a kan mulki ba. Alhalin su ma an zabo su ne daga cikin talakawa, sun kuma san irin yadda talakawa ke ta kokawa da wahalhalun da suka shiga sakamakon tsauraran matakan da gwamnatin baya ta rika dauka a cikin tsare-tsarenta na inganta tattalin arzikin kasa. Amma sai gashi su ne gaba-gaba wajen kulla yadda za su ci amanar talakawa da aka ba su, don arzuta kansu da ‘ya’yansu. Wannan babban abin kunya ne gaskiya, wanda ya kamata gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta tashi tsaye ta maganceta tun kafin wankin hula ya kai ta dare.
Sauke tsohuwar minista Betta Edu da sanya Hukumar EFCC ta gudanar da bincike na musamman kan wannan al’amari abin a yaba ne sosai. Da fatan kuma gwamnati za ta sake watsa komarta ga sauran ma’aikatu da hukumomin gwamnati game da yadda suke sarrafa kudaden da ake ba su na kasafin kudin gudanar da ayyukansu.
