Ƙungiyar masu shirya fina-finai ta ƙasa (MOPPAN) ta gurfanar da wani matashi mai suna Ahmad Pasali a gaban kotu bisa zarginsa da kalaman ɓatanci da kazafi da ya yi kan wasu jaruman Kannywood da kuma masana’antar gaba ɗaya.
Ahmad Pasali ya wallafa wani faifan bidiyo a shafukan sada zumunta wanda ya janyo ce-ce-ku-ce, lamarin da ya sa ƙungiyar MOPPAN ta ɗauki matakin maka shi a gaban wata babbar kotu a garin Jos domin fuskantar hukunci.
Tun da farko, kotun Upper Area Court da ke Kasuwar Nama a Jos ta umarci Ahmad Pasali da ya bayyana a gabanta ranar Litinin, 4 ga watan Maris, domin amsa tuhume-tuhumen da ake masa.
Da yake bayani kan lamarin, shugaban MOPPAN na kasa, Malam Maikuɗi Umar Cash Man, ya bayyana cewa sabon shugabancin ƙungiyar ba zai lamunci duk wani yunƙurin ɓata suna ko cin zarafin ’yan masana’antar Kannywood ba.
