Daga USMAN KAROFI
Ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Ata, ya zargi mataimakin gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, da rashin girmama Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa ministan kan harkokin watsa labarai, Seyi Olorunsola, ya fitar, ya ce mataimakin gwamnan ya yi wata magana da ba ta dace ba kan rikicin sarautar Kano, inda ya ƙalubalanci Tinubu da ya je ya sauke sarkin da ya naɗa kuma ya ajiye a maƙabarta.
Ministan ya bayyana wannan kalami a matsayin mai tada zaune tsaye da kuma rashin ƙwarewa.
Ya ƙara da cewa wannan ba shi ne karon farko da gwamnatin Kano ke nuna rashin biyayya ga doka da kuma rashin girmama cibiyoyin dimokuraɗiyya ba.
A cewarsa, rikicin sarautar Kano yana gaban kotu, don haka bai kamata wani ya rika yin furuci da ka iya gurɓata shari’a ba.
Ministan ya buƙaci mataimakin gwamnan ya janye wannan magana cikin awanni 72, sannan ya nemi afuwa daga Shugaba Tinubu.
Ya kuma gargaɗi gwamnatin Kano da ta bi matakan shari’a wajen warware matsalolinta, maimakon cin zarafin shugaban ƙasa da girmamawarsa.
