Gwamnatin Tarayya ta yi alƙawarin samar da wadatacciyar wutar lantarki a Ramadan

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ministan Wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya alƙawarin cewa za a samu isasshen wutar lantarki a watan Ramadan wanda aka fara a ranar Asabar.

A saƙonsa ga al’ummar Musulmi, Ministan ya ce yana sane da ƙalubalen da ƴan Nijeriya suke fuskanta kan rashin wadatacciyar wutar lantarki.

Ya ce, lallai musulmai suna buƙatar ƙarin adadin lantarki acikin watan azumi, wanda a saboda haka ne suke ƙoƙarin samar da isasshen wutar a yanzu da ma nan gaba.

Ya kuma ce, Gwamantin Tarayya tana ƙoƙarin shawo kan matsalolin ɗaukewar wuta a sakamakon lalacewar rumbun lantarki na ƙasa tare da ake samu akai-akai da kuma bunƙasa ɓangaren.

Ministan ya yi kira ga al’ummar musulmi su yi amfani da wutar yadda ya kamata tare da kiyaye haɗurran da take da su.

Haka kuma ya nasihance su da su yi amfani da damar watan wajen karatun Al-ƙur’ani mai girma da yaɗa kyautayi a tsakanin su gami da taimakon mabuƙata.

By Babaji