Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya ce shi burinsa ya zama gwamnan Kano ba sake zama shugaban jam’iyyar APC ba a jihar ta Kano.
Abdullahi Abbas ya shaida wa BBC hakan ne yayin mayar da martani ga ministan ma’aikatar gidaje na Nijeriya, Yusuf Abdullahi Ata kan kalamansa na baya-bayan nan inda ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar.
Ministan ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar APC muddun aka sake zaɓen shugaban jam’iyyar na Kano, Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar a karo na huɗu.
A yanzu haka zafafan kalaman ministan a wani bidiyo sun karaɗe shafukan sada zumunta, wanda wani abu ne da ke ci gaba da tayar da ƙura a siyasar jihar Kano.
Sai dai shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya shaida wa BBC cewa Yusuf Ata ‘ba ɗan jam’iyyar ba ne’ sannan sun yi mamakin dalilan da suka sa aka ɗauko shi har aka ba shi muƙamin minista.
”Mu a wajenmu ‘yan jam’iyya, dama ban ɗan jam’iyya ba ne, a Kano gaba ɗaya a ƙaramar hukumarsa ne mu ka yi na uku.
”Kuma ba mu sani ba aka bashi minista kuma har shugaban ƙasa mu gaya wa cewa ba ɗan jam’iyyarmu ba ne, anti party ya yi mana” inji shi.
Hon Abbas ya ce sun yi mamakin muƙamin minista da shugaba ƙasa ya ba shi.
”Muna mamakin yadda aka yi wannan abun wallahi, ɗan siyasa ne na ƙaramar hukuma kawai”
Wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, ya nuna ministan ma’aikatar gidaje, Yusuf Abdullahi Ata yana jawabi a tsaye ga magoya baya inda ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar APC a Kano shi da magoyansa matuƙar ba a sauya shugabancin jam’iyyar a jihar ba.
Ministan ya ce furucin jagoran jam’iyyar ne ya jawo faɗuwar jam’iyyar a zaɓen da ya gabata na 2023, kamar yadda ya bayyana a taron masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumarsa ta Fage a jihar Kano.
Ata ya ce, “muna faɗa wa kowa, idan aka mayar da irinsu, duk irinmu fita za mu yi.”
Ya ƙara da cewa, “mu an mana tarbiya, mun san waye malami, mun san waye babba. Saboda haka ba za mu sauka daga turbarmu ba. Idan suka dawo da shi, mu za mu fita, kuma na rantse da Allah sai jam’iyyar ta sake faɗi zaɓe,” in ji shi.
“Dole a canja, dole a nemo mutanen kirki masu mutunci a ba su saboda ya zama tare da mu, ya yi sha’awar ya sake ba mu.”
Da alama dai wannan sabon rikici da ya kunno kai a jam’iyyar ta APC a jihar Kano na kara fito da irin rarabuwar kai da takun tsaka a tsakanin ‘yayan jam’iyyar da kan iya shafar tasirin jam’iyyar a jihar ta Kano.
