MOPPAN ta miƙa ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Ƙungiyar masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, ƙarƙashin inuwar MOPPAN, ta miƙa ta’aziyyarta ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, Masarautar Kano, da dukan iyalan sarauta bisa rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi.

A cikin wata sanarwa da Ibrahim Amarawa, jami’in hulɗa da jama’a na MOPPAN, ya fitar, ƙungiyar ta bayyana rashin marigayin a matsayin babban rashi ba kawai ga Masarautar Kano da jihar ba, har ma ga Najeriya gaba ɗaya.

MOPPAN ta yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin, ya ba iyalansa da ‘yan uwa da al’ummar Kano haƙurin jure wannan babban rashi.

By ukarofi