Janar Tsiga ya kuɓuta bayan kwana 56 a hannun ‘yan bindiga

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), tsohon darakta Janar na shirin NYSC, ya samu ‘yanci bayan shafe kwanaki 56 a hannun ‘yan bindiga. An sace shi ne a garinsu da ke ƙaramar hukumar Bakori a Jihar Katsina ranar 5 ga Fabrairu, tare da wasu mutum tara.

Bayan da iyalansa suka biya kuɗin fansa, masu garkuwar sun ci gaba da tsare shi na tsawon makonni. Akwai rashin jituwa kan adadin kuɗin da aka biya, inda wasu ke cewa Naira miliyan 60 aka biya, yayin da wasu majiyoyi ke cewa adadin ya ninka hakan sau uku. Majiyar daga danginsa ta bayyana cewa bayan an miƙa kuɗin, masu garkuwar sun ɗauki mako guda kafin su kira danginsa tare da ba su damar jin muryarsa.

Wani babban jami’in soja ya tabbatar da sakin Tsiga, yana mai cewa yana cikin ƙoshin lafiya. Haka nan, wasu majiyoyi daga danginsa sun bayyana cewa an sako shi daga Jihar Zamfara, kuma ana shirin kai shi Abuja. Wannan na zuwa ne bayan an ƙi ƙara biyan kuɗin fansa da ‘yan bindigar suka buƙata a ƙarin lokaci.

By ukarofi