Daga UNCLE LARABI
Al’adar ɗan adam ce idan ya rabu da mutum daga baya ya zo yana begen sa komai wahalar kuwa da ya ba shi ko ya saka shi a ciki.
Wannan masifar ita ce ta bibiyi ’yan Nijeriya tun daga 1983 har zuwa 2003 da mu ka yi ta marmarin Marigayi Buhari ya dawo mulkin Nijeriya. Bayan a can baya Iyayenmu da yayyenmu sun faɗa mana irin baƙar wahala da azabar da suka sha a ɗan ƙaramin mulkinsa da ya yi na soja.
Sun sha wahala wajen canjin kuɗi (da ya dawo mulkin muna da wayo da hankali mu ma mun sha wannan wahalar har kwana aka dinga yi a ATM, wanda zai baka N5000 ‘cash’ har ganin ƙimarsa ka ke yi).
Sun sha wahala wajen kasuwanci. An karya wasu da yawan ’yan kasuwa aka dinga faɗa ‘stores’ ɗinsu. Da wayonmu da hankalinmu hakan an maimaaita tunda an rufe mana ‘Boarder’. Kasuwancin ya gagari da yawan mutane sakamakon karyewa Naira a idon duniya.
Abinci ya yi tsada har ta kai iyayenmu na cin tuwon fulawa. Da wayonmu an zo ana cin Rai-ɗore da tafasa da shinkafa irin wadda ake ba wa doki wadda ake yi wa laƙabi da Afafafa.
Har yanzu wannan abun da muka gani da alama bai ishe mu hankali da izina ba. Muna sake ƙara son mu jawo wa kanmu wata jangwangwamar.
Jonathan mun manta mulkinsa ne da kusan duk da hankalinmu da wayonmu ya yi nasa mulkin?
An sha wahala wajen yaƙi da Boko Haram. Bom ya dinga tashi ko’ina a Arewa. Ba mu da tabbas a kasuwa ko a wajen bauta; masallatai da coci. Babu da sukuni ko nutsuwa a danjojin bada hannu ko cikin go slow. Hatta a gidajenmu ba mu da aminci da baƙo ko baƙuwa, musamman wanda ba ka sani ba.
Kabilanci ya taka gudummawa a wancan lokacin. Amma duk mun manta muna son ya ƙara dawowa ya sake gasa mana wata sabuwar ayar a hannu. Sai kuma shi ma mu fito mu ƙara zagin sa. Akwai abubuwa da yawa na matsalolin mulkin Marigayi Buhari da na Goodluck Jonathan waɗanda ban faɗe su ba, amma da yawanmu mun san su. Don haka mu taimaka mu daina yaudarar kanmu don kewa ta ɗebe mu, mu sake dawo da bara bana.
Jonathan yana nan a Jonathan ɗin da muka zaga a 2009 zuwa 2015. Nigeria ma tana nan a yadda take ba ta canja ba. Idan har muka yi gigi da rawar kan sake dawo da Jonathan mulkin Nijeriya, to duk abin da ya biyo baya kada mu zo muna zagin sa. Bai manta Komai a Villa ba. Ku bar shi ya ci gaba da zamansa da sauran mutuncinsa a matsayinsa na tsohon Shugaban ƙasar Nijeriya, wanda ya miƙa mulki lokacin da yake da damar murɗe zaɓen da aka yi a 2015 ko da kuwa kowa zai rasa ransa a Nijeriya. Amma ya zaɓi zaman lafiya, wanda hakan shi ne babban abin da ya siya masa mutunci a idonmu.
To, a taimaka a bar shi da wannan mutuncin da ƙimar. Kar a yaudari kai a sake dawo da shi mulkin Nijeriya. Gara ya mutu da waccan darajar da ƙimar da ya sake dawowa mulkin Nijeriya, idan aka samu akasi ya mutu da mummunan baƙin kinin da za mu zo muna zagin sa muna cewa ba za mu yafe masa ba.
Uncle Larabi, wanda ake kira da Abdullahi Jibril Dankantoma, marubuci ne a Kano, kuma za a iya samun sa a 08065418892
Lahadi, 17 ga Agusta, 2025.
