Yadda ’yan Arewa suka fi tururuwar neman aiki

Spread the love

Daga ABDUL’AZIZ ABDUL’AZIZ

Neman wani bayani ya kai ni shafin daukar ma’aikata na su Civil Defence da Immigration wanda aka rufe a satin nan. Kawai sai na ci karo da bayanan da suka fitar na masu neman aiki. Jaddawalin abu ne mai ɗaukar hankali ko ma tada hankali. Ya tuna min wata tattaunawa da muka yi kwanannan a shafin Prof Abdulrazak Ibrahim akan matsalolin yankin Arewa, musamman yadda muke barin jaki kullum ana dukan taiki.

A cikin jihohi goma mafiya yawan masu neman aiki (applicants) jihohin tara na farko duk na Arewa ne; ta 10 ɗin ce kawai daga Kudu (Oyo). Jihar Kogi ce ta farko da masu nema dubu 116 sai Kaduna, sai Benue, sai Kano ta huɗu da applicants sama da dubu 89.

Babban abun lura shi ne jihohin Lagos da Rivers waɗanda su ma masu yawan mutane ne amma sai ga shi su ne na can ƙarshe wajen yawan masu neman waɗannan ayyuka. Lagos da take biye da Kano wajen yawan jama’a ita ce ta biyun ƙarshe wajen masu neman wannan ayyukan da yawan applicants dubu 14. Rivers da take ta takwas a yawan jama’a ita ce ta ukun ƙarshe a wannan jadawali da applicants dubu 22 da ƴan kai.

Kodayake ni ba masalin tattalin arziƙi ba ne amma daga gani wannan jadawali yana nuna ƙarara matsalar rashin aikin yi da talauci tare kuma da ƙarancin dama ta dogaro da kai. Wannan ya fito da gazawarmu a matsayin al’umma. Gazawar gwamnatocin mu na jihohi wajen kyautata tattalin arziƙinmu da gazawar masu hannu da shuni wajen samar da hanyoyin samar da ayyuka (saɓanin zama masu sayar da kayan da aka yi a wasu wurare) ya kuma fito da gazawar matasanmu wurin jajircewa da tsayawa da kai wajen nema maimakom tunanin aikin albashi a kodayaushe.

Wannan kawai ɗan tsokaci ne na san masana za su iya wa’azantar da mu sosai daga sharhin waɗannan alƙaluma.

“Mu tashi mu farka ƴan Arewa, mu san bacci aikin kawai ne” – Dr Mamman Shata Katsina

Abdul’aziz Abdul’aziz mai taimaka wa Shugaban ƙasa Kan Harkokin Yaɗa Labarai ne

By ukarofi