Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Akwai wani Sarki da ke da wasu murguza-murguzan karnuka da ya ke kiwatawa ba don komai ba sai domin jefa bayinsa da su ka ci amanarsa, su yi kalaci da su.
Wata Rana wani babban hadiminsa ya yi wa Sarki laifi wanda bayan amsa laifinsa sai Sarki ya yanke masa hukuncin cewa a jefa shi gidan karnuka su yi kalaci da shi. Wannan bawa ya ce ya na da magana.
“Saboda tsawon shekaru goma da na shafe a fadarka ina maka hidima, don Allah a jinkirta aiwatar min da hukunci sai bayan kwana goma”
Nan da nan Sarki ya aminta da bukatar ya ce a kyale shi sai bayan kwana goman. Shi kuwa gogan naka, bai zame ko ina ba sai garken da ake ajiye wadannan karnuka. Ya ce da Mai tsaronsu, nazo ne domin kawai na hidimtawa wadannan karnuka kafin kwanaki na goma su cika. Mai gadin karnuka ya cika da mamaki. Shi kuwa ya ci gaba da kula da karnuka ya na kawo musu abinci da nama da ruwa, har wanka ya rika yi musu.
Da kwanaki goma su ka cika, Sarki ya sa aka kamo mutumin don zartar masa da hukunci. Da aka je aka jefa shi cikin dakin karnuka, sai aka ga sun yo caa kansa suna kada masa jela suna lashe shi cikin murna.
Da aka gayawa Sarki, ya cika da mamaki ya ce a je a zo da shi.
“Me ya faru karnuka ba su cinye ka ba?” “Ko kana da wani lakani ne?”
“Ranka ya Dade, na yi wa wadannan karnuka bauta ne ta kwanaki goma kacal, amma ba su manta da ita ba, kai kuma shekaru goma na yi ina bauta maka, amma kuskure na farko ka ce a kashe ni”
Darasi
Dan Adam na iya juya maka baya a kowane lokaci ba tare da la’akari da girma ko dadewar gudunmuwar da ka ba shi ba. Don haka kada ka cika tsammani daga kowane mahaluki sannan duk abinda zaka yi, yi don Allah kadai shine ba ka da nadama.
Malam Ali mai sharhi ne kan harkokin yau da kullum kuma mazaunin Kano
