Mu ji tsoron wutar Jahannama

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIƙ

Wannan hoto, tumbin duniya ne da irin narkakkiyar wuta da ke ci a ƙarƙashin ƙasa, wadda zafin wannan wutar ya zarta zafin da Rana ke da shi. Zafin wutar da ke tumbin duniya kuma muke taka doronta, ya kai kimanin degree 6000 na Celsius, yayin da zafin Rana degree 5500 ne.

Idan za ka iya kwatanta wannan zafi da abinda ka sani, sai ka ce ya kai zafin ninkin tafasashshen ruwan-zafi (wanda 100° Celsius ne) sau 60 kenan. Ka duba yadda tafasashshen ruwan zafi ke kwashe fatar mutum nan take. To, Ina ga idan an ninka wannan zafin sau 60?

Allah na fito ma na da wannan narkakkiyar wuta da ke tumbin duniya lokaci-lokaci, yayin girgizar ƙasa ko aman wutar dutse (ɓolcanic eruption) duk inda kogin wannan narkakkiyar wuta ya bi, sai ya narke komai a kan hanyarsa, walau dutse ko ƙarfe.

Wannan fa zafi ne na wannan duniya, ba irin na Jahannama ba. Idan ba ka tsoron Allah ma, to ka ji tsoron Jahannama, kuma kwana nawa ya rage mana zuwa lahira?

Duk tsiyarka, nan da shekaru, matuka, shekara 100 ka san sai buzun ka wallahi, kowane ne kai. Idan ka ga dama, ka yi alheri, in ka ga dama yi ta aikata sharri. Kai kadai aka haifa, kake rayuwa, za ka mutu a saka ka kabari kai kadai, kuma kai kadai Allah zai yiwa hisabi ranar lahira. Ko aljanna, ko wuta…zabi ya rage namu.

A yi gaskiya, a kare gaskiya sannan a aikata ta. Ko kuma a bi karya, a kare ta tare da aikata ta. Akwai ranar murna ko ranar ƙin dillanci. Imma shakiran, wa imma kafura!!!

Sadiƙ manazarci ne a Kano

By ukarofi