Akwai barazana ga ƙasar da ba ta iya ciyar da kanta –  Obasanjo

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon shugaban ƙasar Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya yi wani kakkausan gargaɗi game da illar da Nijeriya za ta iya fuskanta idan ta kasa bai wa noma fifiko.

Da yake jawabi a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun, yayin ziyarar ban girma da kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman daga jihar Neja suka kai masa, Obasanjo ya jaddada buƙatar gaggauta saka hannun jari a fannin noma.

“ƙasad da ba za ta iya ciyar da kanta ba, tana zaune ne a kan bom, wanda zai iya tashi a kowane lokaci,” Obasanjo ya yi gargaɗin, yana mai jaddada cewa ƙalubalen da aasar ke fuskanta za su ci gaba idan har Nijeriya ta gaza samun wadatar abinci.

Tsohon shugaban aasar ya yaba wa gwamnan jihar Neja Mohammed Umaru Bago kan yadda ya canja salon aikin noma, inda ya nuna kamanceceniya tsakanin ayyukan Bago da nasa na “Operation Feed the Nation” na shekarar 1976.

Obasanjo ya bayyana cewa da zuwan na’urorin noma na zamani, tasirin irin wannan ya haifar a shirye-shirye na iya zama mafi kyawu fiye da na baya.

A wani ɓangare na ziyarar tasu, tawagar ta kuma zagaya wani katafaren gona marar kasa inda ake horar da matasa ‘yan Neja sana’o’in ƙere-ƙere na noma, wanda ake sa ran za a yi amfani da su a faɗin jihar Neja.

Obasanjo ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi la’akari da saka hannun jari a noman da ba ta da ƙasa, yana mai gargaɗin cewa nan ba da daɗewa ba ƙasar za ta iya fuskantar ƙarancin filayen noma saboda yadda ake amfani da filaye a halin yanzu.

Ya jaddada cewa ɗaukar sabbin hanyoyin noma na da matuƙar muhimmanci wajen ɗorewar noma a Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da Aisha Wakaso, mai baiwa gwamnan jihar Neja shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Aisha Wakaso ta fitar, ta yi kira ga sauran gwamnonin jihohin da su yi koyi da jihar Neja wajen bunƙasa noma. Ya kuma ja hankalin jihar Neja da ta ci gaba da saka hannun jari a harkar noma tare da lalubo hanyoyin zamani don inganta ayyukan da ake da su.

Obasanjo ya kuma bayyana aniyarsa ta ziyartar jihar Neja tare da tawagarsa domin koyi da ci gaban da aka samu kawo yanzu da kuma musayar ra’ayoyin da za su bunaasa ayyukansa na noma.

Hauwa Bako, mai ba da shawara ta musamman kuma mai kula da shirye-shiryen zuba jari na zamantakewa, ta yi magana a madadin tawagar jihar Neja. Ta nuna godiya ga tsohon shugaban kasar bisa jagorancinsa, inda ta bayyana cewa ziyarar na da nufin sanin ɗimbin kwarewa da hikimar Obasanjo. 

Bako ya jaddada ƙudirin jihar Neja na bunƙasa harkokin noma da aiwatar da sabbin hanyoyin samar da wadataccen abinci a jihar da kuma ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi