Ƙarancin mai: Sai abinda muke da shi za mu iya bayarwa, inji ’yan kasuwa

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Masu sayar da man fetur sun danganta matsalar ƙarancin man fetur ga ƙalubalen kayan aiki da aka daɗe ana fuskanta.

Shugaban ƙungiyar Masu Kayayyakin Man Fetur, (PETROAN), Billy Gillis-Harry, wanda ya kasance baƙo a shirin Tattaunawar Safiya na Gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin ne ya bayyana hakan.

A cewarsa, masu sayar da mai a halin yanzu su kansu suna fuskantar ƙarancin man, kuma  za su iya bayar da abin da kawai suka samu ne”.

Ya ce, “Har sai mun samu man cikin yalwa za mu iya magancewa tare da fita daga cikin wannan ƙalubale.

“Na yi imanin cewa tabbas kun ji daraktan sadarwa na NNPC wanda ya bayyana cewa har yanzu al’amuran da ke faruwa suna da alaƙa da kayan aiki.

“Don haka har sai sun yanke shawarar, za mu iya kawai sarrafa ɗan kaɗan da suke kawowa, kuma mu ba mu mu rarraba a tsakanin mambobinmu.

“NNPCL yana yin iya ƙoƙarinsa don kawo samfuran, kuma abin da muke da shi ne kawai za mu iya samarwa.”

Lokacin da aka tambaye shi ya ba da ƙarin bayani kan mene ne ƙalubalen ke tattare da shi, ya ce, “Batun shi ne jigilar man. Har sai jirgin jigilar ya sami samfura, ba zai iya isar da shi zuwa kowane ma’ajiyar kayayyaki ba. Kuma har sai rumbunan ajiya sun sami kayayyaki, mu ’yan kasuwa ma ba za mu iya samun damar yin amfani da kayayyakin,”

Sai dai ya ba da tabbacin cewa ‘yan kasuwa na tattaunawa da hukumar NNPCPL kan ƙalubalen samar da man fetur.

Bayanin Gillis-Harry kan ƙarancin ya biyo bayan ƙarancin man fetur, musamman a sassan arewacin ƙasar.

ƙarancin, ya bazu zuwa Legas a aarshen makon da ya gabata.

By ukarofi