Tare da BILKISU YUSUF ALI, Ph’D
Gabatarwa
Tarbiyya ce ginshiƙin rayuwar ɗan Adam, wadda ke tsara halayensa, tunaninsa da mu’amalarsa da sauran jama’a. A cikin addinin Musulunci da al’adun Hausawa, ana ɗaukar tsoron Allah a matsayin tushen kyawawan ɗabi’u da nagartacciyar rayuwa. Tsoron Allah (taƙawa) yana nufin kiyaye dokokin Ubangiji, nisantar haram, da aikata alheri a kowane hali. Tsoron Allah kamar yadda ya zo a hidisi shine “ka bautawa Allah tamkar kana ganinsa don in kai ba ka ganinsa shi yana ganinka” (Au kama ƙalarrasul) Don haka wannan gajeren rubutun zai yi magana ne akan muhimmancin tsoron Allah da iyaye ko makusanta za su yi wajen yin tarbiyyar iyalinsu ko al’ummarsu.
Ma’anar tsoron Allah da tarbiyya
Tsoron Allah shi ne jin tsoron aikata abin da zai sa Allah Ya yi fushi, tare da ƙoƙarin aikata abin da zai jawo yardarsa. Tarbiyya kuwa ita ce koyar da ɗabi’u masu kyau da horar da mutum ya zama nagari a mu’amalarsa.Malamai sun bayyana cewa tarbiyya ba ta cika ba sai an haɗa ta da tsoron Allah, domin shi ne ke hana mutum aikata munanan abubuwa ko da babu mai kallo.
Muhimmancin tsoron Allah a tarbiyyar iyali
1. Gina halaye nagari
Tsoron Allah yana sanya mutum ya kasance mai gaskiya, riƙon amana, da kyawawan ɗabi’u. Yara da aka tarbiyantar da su da tsoron Allah sukan zama masu biyayya da ladabi.
2. Hana aikata laifi
Mutumin da ke da tsoron Allah ba ya aikata laifi ko da yana shi kaɗai. Wannan yana rage sata da zalunci da ha’inci da sauran miyagun halaye a cikin al’umma.
3. ƙarfafa zumunci
Tsoron Allah yana sa mutum ya kula da haƙƙin iyaye da ‘yan’uwa da makwabta, wanda ke haifar da zaman lafiya da haɗin kai.
4. Samar da zaman lafiya a gida
Iyali da ke rayuwa bisa tsoron Allah sukan kasance cikin kwanciyar hankali, domin kowa yana kiyaye haƙƙin ɗan uwansa.
5. Kiyaye mutunci da daraja
Tsoron Allah yana hana mutum aikata abubuwan da za su zubar da mutuncinsa ko na iyalinsa. Wannan kuwa in yana cikin garinsu ne ko yana nesa da gida. Mai tsoron Allah a duk inda ya samu kansa zai yi ƙoƙari ya zama wakilin harshensa da addininsa da al’adarsa ba zai watsar da gida ba da kyakkyawar tarbiyyar da ya samu ba.
Tasirin tsoron Allah ga al’umma
1.Rage laifuka
Al’umma mai tsoron Allah tana da ƙarancin laifuka kamar sata da cin hanci da rashawa da rikici na addini ko ƙabilanci da riƙe amana da sirri da sauran manyan laifuka kamar zina da fyaɗe da kisan kai da sauransu.
2.Inganta adalci
Shugabanni da talakawa masu tsoron Allah suna gudanar da al’amuransu cikin gaskiya da adalci. Shugaba mai tsoron Allah ba zai cutar da waɗanda ke ƙarƙashinsa ba da zalunci da cusgunawa haka su ma talakawa da suka shawu da tsoron Allah ba za a gansu a wurin tawaye da yarfe ko ƙazafi ko yaɗa jita-jita da tayar da zaune tsaye ba.
3.Haɗin kai da cigaba
Tsoron Allah yana ƙarfafa haɗin kai, wanda shi ne ginshiƙin cigaban kowace al’umma. Duk al’ummar da kanta ya haɗu za a same ta tana da tarbiyya da zaman tare da kare haƙƙin juna sannan wannan al’ummar ba za a ganta wurin aikata manyan laifuka ba don bakinta a haɗe yake wurin kawo gyara ba ɓarna ba.
Hanyoyin gina tsoron Allah a zukatan yara
1.Koyar da su addini tun suna ƙanana. A shayar da su madarar addini komai ake kafa musu hujja daga addini sannan ake nuna musu falalar zama na gari da illar zama mutumin banza tun suna ƙanana da tanadin da Allah ya yi wa nagartattu da wanda ya yi wa waɗanda suka saɓa.
2. Zama abin koyi daga iyaye
Iyaye dole su zama masu tarbiyya da koyi da kyawawan ayyuka a idon ‘ya’yansu duk abin da za su aikata su yi ƙoƙari su yi mai kyau don yaransu su gani su aikata.
3. Koyar da su sakamakon alheri da hukuncin laifi
Iyaye su nunawa yaransu duk aikin alheri yana da sakamako haka duk aikin sharri akwai sakamakonsa tun a duniya haka a lahira.
4.Kula da irin abokan da suke hulɗa da su
Yawanci wasu halaye da yara suke ɗauka ya danganta da irin abokan da suke mu’amala ne da su. Don haka kai da ka ke yi wa ɗanka tarbiyya ya zama wajibi ka sa ido akan abokan ɗanka in ma da hali ka jajirce ka zaɓa masa abokan da ka ke ganin sun dace da shi a mu’amala.
Yawaita tunatar da su game da Allah da ayyukan alheri
Ya zama mafiya yawan hirarku kuna tunatar da yaranku ayyukan alheri da wasu magabata suka aikata da kuma irin kyakkyawan sakamakon da suka samu a cikin hikima da azanci.
Kammalawa
Tsoron Allah shi ne tushen kyakkyawar tarbiyya a cikin iyali da al’umma. Duk wata tarbiyya da ba ta ginu a kan tsoron Allah ba, tana da rauni kuma ba za ta daɗe ba. Don haka wajibi ne iyaye da shugabanni su mayar da hankali wajen koyar da tsoron Allah domin samar da al’umma mai nagarta da zaman lafiya.
Manazarta:
Al-ƙur’ani mai girma
Sahih al-Bukhari
Sahih Muslim
Imam Al-Ghazali – Ihya Ulum al-Din
Ibn Qayyim al-Jawziyya – Madarij al-Salikin
Abdullahi Smith (1978) – Islam in Nigeria
Hiskett, M. (1984) – The Deɓelopment of Islam in West Africa
Fafunwa, A. B. (1974) – History of Education in Nigeria
Gusau, S. M. (2013) – Tarbiyya a Musulunci
