Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya tabbatar da cewa dakarun Amurka da na Nijeriya sun yi nasarar halaka Abu-Bilal al-Minuki, wanda aka bayyana a matsayin mataimakin shugaban ƙungiyar ISIL a matakin duniya, a wani farmakin haɗin gwiwa na yaƙi da ta’addanci da aka gudanar a Nijeriya.
Trump, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, ya bayyana cewa an shirya aikin cikin tsari mai inganci, tare da yabawa haɗin gwiwar dakarun Amurka da rundunar sojin Nijeriya wajen bin diddigin tare da kawar da jagoran ’yan ta’addan.
Haka kuma, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba da nasarar, yana mai bayyana ta a matsayin misali mai ƙarfi na haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashe, tare da jinjinawa ƙwarewar jami’an da suka gudanar da aikin.
Ya nuna kwarin gwiwa cewa wannan nasara za ta buɗe ƙofa ga ƙarin hare-hare na musamman kan cibiyoyin ’yan ta’adda a faɗin ƙasar.
Bayanan leƙen asiri da aka tattara daga Cibiyar Yaƙi da ’Yan Ta’adda, wato Counter Extremism Project, da sauran rahotannin tsaro sun bayyana muhimman abubuwa 10 game da Abu-Bilal al-Minuki kamar haka:
1. Ya kasance ɗan Nijeriya da ke aiki a yankin Sahel.
2. An san shi da sunaye daban-daban ciki har da Abor Mainok da Abubakar Mainok.
3. An haife shi a shekarar 1982 a Mainok, yankin Benisheikh a Jihar Borno.
4. Ya kai matsayin jagoranci a ISIL bayan kisan Mamman Nur a 2018.
5. An bayyana shi a matsayin mai tsattsauran ra’ayi kuma muhimmin jigo a Yammacin Afirka.
6. An ce yana da saɓani da Abubakar Shekau kan jagoranci da tasiri.
7. Rahotanni sun nuna ya taimaka wajen tura mayaƙa zuwa Libya a 2015–2016.
8. Ya yi aiki a ofishin ISIL na al-Furqan da ke tsara ayyukan yanki.
9. Amurka ta ayyana shi a matsayin ɗan ta’adda na duniya a 2023.
10. An alaƙanta shi da harin sace ’yan mata na Dapchi a 2018.
Daga ɗan leƙen asiri zuwa kwamandan ISIL a Yammacin Afirka: Tarihin Abu-Bilal al-Minuki:
Rahotanni sun nuna cewa Abu-Bilal al-Minuki, wanda aka kashe a farmakin haɗin gwiwa na Nijeriya da Amurka, ya taɓa kasancewa ɗaya daga cikin manyan kwamandojin Boko Haram kafin ya yi mubaya’a ga ISIL a 2015.
Sojojin Nijeriya sun bayyana shi a matsayin muhimmin jigo a ayyukan dabaru da tsare-tsaren ƙungiyar, musamman a ɓangaren yaɗa bayanai, yaƙin tattalin arziki da kuma ƙera makamai.
Rundunar sojin ta bayyana cewa mutuwarsa ta rushe wata muhimmin cibiyar da ISIL ke amfani da ita wajen daidaita ayyukanta a sassa daban-daban na duniya.
Ta kuma ce ya jagoranci ayyukan ISIL a yankin Sahel da Yammacin Afirka, ciki har da hare-hare kan ƙananan al’ummomi masu rauni.
A shekarar 2018 kuma, an alaƙanta shi da sace ɗalibai fiye da 100 a Dapchi, Jihar Yobe.
Tsohon jami’in Hukumar Tsaro ta DSS, Dennis Amachree, ya ce kisan al-Minuki zai haifar da babban giɓi a shugabanci da tsarin kuɗi na ISWAP.
Ya ce, “Za a samu babban giɓi a jagoranci da kuɗin ISWAP, saboda yawancin manyan mayaƙa sun mutu tare da shi.”
Ya ƙara da cewa, za a iya samun rikici na cikin gida kan wanda zai gaje shi, ganin yadda yake sarrafa hanyoyin kuɗi da haɗin gwiwar ƙasashen waje.
Masana tsaro sun bayyana cewa duk da muhimmancin aikin, ƙungiyoyi irin ISWAP na iya sake farfaɗowa saboda tsarin su na da rassa da yawa da ke aiki ba tare da cikakken tsari guda ɗaya ba.
Wasu rahotanni sun kuma nuna cewa an taɓa sanar da mutuwarsa a 2024 bayan wani farmaki a Kaduna, amma daga baya ƙungiyar ta ci gaba da ayyukanta.
Masana tsaro daga Turai da Afirka sun bayyana cewa irin waɗannan nasarori suna da tasiri na ɗan lokaci ne kawai idan ba a katse tushen tallafin ƙungiyoyin ba.
Sun kuma yi nuni da cewa matsalar garkuwa da mutane da neman kuɗin fansa na ci gaba da ƙara ƙarfafa ƙungiyoyin ta’addanci a yankin.
A cewarsu, har sai an magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro a ƙasa, ana iya ci gaba da samun irin wannan zagayowar rikici.
Duk da haka, Shugaba Tinubu ya bayyana godiya ga haɗin gwiwar Amurka, yana mai cewa za a ci gaba da ƙarfafa ayyukan haɗin gwiwa kan ta’addanci.
