Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Tun ’yan bazata na nanata kalmomin batanci da a ka lakkana mu su na jifar waɗanda a ke son su tunzura don kyasta ashana ga Arewa amma yayyafi daga Allah ya kwantar da ƙurar, yanzu mutanen sun shiga babin murde wuyan tarihin tushen Musulunci don mabiya su koma harkar fifita ƙabilanci kan addinin.
Da zarar Musulmi sun jingine girman darajar mika wuya 100% ga umurnin Allah sun koma son zuciya ta ƙabilanci to sun gama yawo don ƙarshe a ka iya shigo da addinin nan na BA ALLAH a dakatar da mutane daga sallah, azumi da zakka. Aikin hajji ma kwanan nan ya fara samun suka daga ‘yan bazata.
A wannan lokaci da wasu su ka karɓo kwangila don rusa Arewa ta hanyar sanya rigar karya ta Hausawa alhali sam ba ma Hausawa ba ne, ya zama mai muhimmanci mu riƙa haskawa jama’ar da a ke son a rudar don kar su wayi gari su na ɗauki ba daɗi da juna a sanadiyyar makircin annamimai. Ba nan wadannan ‘yan bazata su ka tsaya ba, sun ma dau alamu da mayafin musulunci sun yafawa kansu don samun saukin wannan yaudara. Ba zai yiwu mu bar masu zuciyar da ta kekashe su cuci jama’a da wannan mugun kamfen din na cusa kabilanci a ƙalubalen Arewa don wargaza ‘yan uwantakar Musulmi.
Ta ina zai zama Bahaushe a nan Arewa don zangar zai faɗi ra’yinsa sai ya kirkiri suna da shafin bogi ya yi amfani da hotunan ARTFICIAL INTELLIGENCE ya kuma murde tarihi. Wallahi mutranen nan sun san abun da su ka karɓo na makirci don haka su ke zama a ɓoye ruff a wayar salula. Ina ma mamakin yadda kamfanin META ba zai ɓullo da manhajar da za ta daƙile duk wani mai murdiya daga buɗe shafi ba. Akwai buƙatar mutum ya miƙa lambarsa ta NIN ko BVN kafin samun damar buɗe shafin yanar gizo. In ba tsoro ba su fito fili.
Wallahi ba yadda za a yi musulmin kwarai ya fifita ƙabila a kan addinin Allah. Don haka mutanen nan sun tabbata ‘yan bazata kuma tabbas ko za su murde yanar gizo gaba daya ba za su yi nasara ba don addinin Allah su ke kai wa farmaki.
Zuwa yau da na ke rubutun nan, mu na ƙara godewa Allah don ba wani dattijo ko mutumin kirki da ke cikin wannan harkar. Ba malamin kirki da zai koma ya na batun wai ƙabilar nan ko ƙabilar can, sai yi wa duk mabiya gargaɗi na kaucewa zalunci don Allah ya na madakata don jiran dukkan mujirmai.
Kai ai in wani ya na mamakin yadda ‘yan bazata su ka yi tsalle su ka ɗirka kan tarihin Annabi SAW ban da irin mu! Yo ai rago ne da wutsiyar kare. Kai ‘yan bazata fa kan iya basaja su yi kamar su na sallah amma carman dudu su ke karantawa. Hi ho hai su kan iya zuwa aikin hajji amma yawon leƙen asiri da bude ido su ke zuwa. Na ga wani ma mai damƙar karnuka don bai taɓa yin alwala da hannun ba, ya na batun Manzon Allah! Za su yaudari wasu amma mun riga mun jefa sufana a injin motarsu dole ta kakare a bakin danja.
Mutum da dambajejen bakinsa ko ma ya na Larabci ko jan hadisi da fassarar gatari duk ba tabbacin musulunci ba ne. Ba ta yadda za a yi wani ya ja hadisin Manzon Allah ya ba da kariya ga ƙabilanci.
Yo in ba ƙarfin hali ba wai ɓarawo da sallama, ta yaya wanda bai shiga Musulunci ba zai yi iƙirarin wai a yanzu an daina yaudararsa da Musulunci. Yanayin kalmomin kawai na nuna a na yaudara da Musulunci na tabbatar da waɗanda ke fadar haka ba layinsu ba ne kuma ba su da alaƙa da wannan addinin.
‘Yan bazata sun fara ambatar hakan don zagin Shehu Mujaddadi da nuna tarihin karantarwarsa kamar ƙarfa-ƙarfa a ka yi wa musamman al’ummar Arewa da a ka same su da addini. Shi kansa Shehun da al’ummar da kowa a lokacin duk ‘yan wannan yankin ne na Arewa don haka ba wanda ya zo daga birnin Kib ko ƙasar Yajuju-wa-Majuju don yaudarar wani. Aiki ne da Shehu ya yi ƙarara ga shi nan a littattafai na bunƙasa addinin Musulunci da kawar da sakarci da tsafi.
Tabbas waɗannan mutanen masu wannan kamfen ba su da ruhin musulunci don haka zagi, kazafi da murɗe wuyan tarihi kan lamura na addini ko ma kan ayyukan Shehu a keɓance ya zama jigon wulakancinsu.
Yayin da ‘yan bazata ke shakiyanci wai a na kwatanta Shehu da Annabi SAW sai kwatsam a ka yi wayi gari su ka ce musuluncin ma bai wanzu ba in ba don an yi aiki da ƙabilanci ba. Ko kunya ba su ji ba na mannawa tarihin Manzon Allah batun alaka da ƙabilanci. ‘Yan bazata sun manta cewa su na karya cewa su Musulmi ne don haka ba su duba yadda Manzon Allah ya zayyana ƙabilanci da abu mai muni ba. Wani mai iƙirarin Musulunci ya danganta abu mai muni ga tarihi mai tsarki na Manzon Allah. Wallahi wannan ba ɗabi’ar Musulmi ba ne. ‘Yan bazata sun tonawa kansu asiri.
Ajandar ‘yan bazata ta kara fitowa fili tarwal kuma hatta waɗanda a baya ke yi wa lamarin kallon surutan soshiyal midiya ko wai matsalar ‘yan bindiga ta kawo hayaniyar; yanzu ya gane maƙiya Allah da Manzonsa ne ke wannan shigar burtu don ci da kudundune kulba na ɓarna a na cewa jaba ce.
Duk makiyin Musulunci na jin haushin yadda a kan tsokani Arewa ta kowace fuska amma yankin a karshe ya zauna daram don hatta Ojukwu da ya ayyana ballewa daga Nijeriya don haushin ba gaira ba dalili na Arewa da ‘yan Arewa ne ya haddasa abun da ya aikata kuma Allah ya ba wa Arewa nasara, dakarunta su ka yi kundunbala su ka wargaza sojojin aware Nijeriya ta sake dunƙulewa.
Hasashe ya tabbata na inda ‘yan bazata su ka nufa daga zagin Shehu Mujaddadi da ya sadaukar da rayuwarsa kakaf kan jaddada addinin Musulunci. Da farko sun fara daga zagin kasuwa da laƙaba miyagun sunaye kan Shehu Mujaddadi zuwa wasu manyan malaman Musulunci da kawar da kai 100% ga duk shugabannin wasu addinai. Miyagun ‘yan kwangilar rusa Arewa sun gaza hakuri da iya kan masu Tauhidi na Nijeriya sun koma kai tsaye kan Annabi SAW. Tsaurin rai na zuga mutanen nan inda ƙarara su ke yayata cewa wai in ba da kabilanci ba, Musulunci ba zai wanzu har mu same shi ba!. Karya su ke da murɗe wuyan tarihi don sam-sam ba a taɓa yin wani abu mai kama da haka ba.
Manya a kwangilar ta bazata sun koma gefe tun da sun gano yadda su ka zunguro sama da sanda, yanzu sun bar ‘yan lakada-kawas masu zunduma ashar sun karbi fagen da caccakar duk wanda ke fito da gaskiya tsantsa. Haka kawai dan sullutun yaro da ko majina ba a gama share ma sa ba, amma zai dubi sa’an mahaifinsa ya surfa ma sa ta Maguzawa.
Ba za a mu taba yin shiru mu bar gungun masu yaƙi da Musulunci su ci karensu babu babbaka ba. Duk surutun da su ke yi don hargitsa Arewa ba zai taba yin nasara ba. In Allah ya yarda za mu cigaba da riƙe tocila mai batur 18 mu haska miyagu a gansu a siffarsu ta gaskiya.
Gaskiya su shafawa kansu ruwa don duk rashin kunyar mutum a nan dai Arewa ko ya sha giyar wake, ba zai aibata tarihin Manzo SAW ya yi tsammanin zai sakata ya yi rawar banjo ba. Kul.
Idan mun dau boye suna da hoto ko adireshi kaɗai da ‘yan karyar Hausa zalla ke yi a shafukan yanar gizo, ya isa fahimtar muguwar manufarsu ga al’ummar Arewa. Ta yaya mutum zai buɗe shafin karya shi kansa matsoraci ne wai a hakan gwagwarmayar kwatar haƙƙin wasu ya ke yi?.
Duk wanda za mu cigaba da iya saurara a mutanen nan sai wanda ya bayyana nasabarsa da Hausawa da sunan Dagacinsu. Duk wanda ya gaza yin haka amma ya buge da ɓoye kansa ya na bakar magana mun san munafuki ba Bahaushe ba ne dan zagon kasa ne ga Hausawa Musulmi. Ba Bahaushe na gaskiya a duniyar nan da za a ce ma sa da ƙabilanci Musulunci ya wanzu a zamanin Manzo ya yarda har ma da kambama iƙirarin da ma zagin wanda ya ce hakan farmaki ne kan tarihin Musulunci.
Ba mamaki a samu wasu ƙalilan da za su ce ai ga su nan a fili kaza da kaza, shin su nawa ne gaba ɗaya kuma mai ya sa su ke hulɗa da haɗa baki da boyayyu makirai su na zagin masu mutunci? Idan ka ce ba ka zagin kowa amma idan boyayye ya yi zagi ka na jin daɗi ka na buga kafa ka na mara ma sa baya, shin kai waye kenan?.
KAMMALAWA
Ina jan hankali a nan ga wasu da su ka rufta don ɗaukar ‘yan karyar Hausa zalla Hausawa ne da su ka fandare, don haka su ke mayar mu su martani a matsayin Hausawa. Hakan babban kuskure ne don ba wani Bahaushen kirki da ke cikin wannan tafiya. Don mutum ya yi ikirarin shi Bahaushe ne, sam ba ya tabbatar da iƙirarinsa sai an tantance aya da tsakuwa.
Na ga sharrin mutanen ma ya sa sun kiɗime inda su kan zargi juna da cewa ba Hausawa ba ne! to ai duk ba Hausawan ba ne gayyar soɗi ne kawai.
