Muhimmancin raya al’adun gargajiya ga rayuwar Hausawa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A cikin wannan mako mai ƙarewa ne al’ummar Hausawa na faɗin duniya, musamman matasa, ɗalibai, marubuta, ’yan jarida da manazarta harshen Hausa suka suka gudanar da bukukuwan tunawa da al’adun gargajiya na Hausawa, a karo na uku cikin bainar jama’a, savanin yadda ake yi a baya ta kafafen sada zumunta a kowacce ranar 26 ga watan Agusta.

Bincike ya nuna cewa, Ranar Hausa ta Duniya ko kuma International Hausa Day a Turance, rana ce da aka keɓance domin nuna muhimmancin harshen Hausa, da tattauna hanyoyin bunƙasa shi da kuma jawo hankali akan irin ƙalubalen da harshen da al’adun gargajiya na Hausawa ke fuskanta. An fara raya bikin ne a shafukan sada zumunta musamman a tsohuwar manhajar Twitter, da niyyar haɗa kan masu magana da harshen Hausa. Kuma an zaɓi ranar 26 ga watan Agusta ne domin tuna ranar da aka qirqiro haruffan “q” da “x” da “v” wanda babu su a haruffan Turanci.

A bana bukin ranar ya mayar da hankali ne wajen tattauna hanyoyin raya kyawawan al’adun gargajiya na Hausawa, don su dace da cigaban zamani. Ta yadda Bahaushe a ko’ina a duniya zai yi alfahari da al’adunsa da harshensa na gado, cikin rubuce-rubucensa, a karance-karancensa, a suturarsa, da abincinsa, da ma duk wata mu’amala da zai yi da sauran jama’a, ta yadda za a gane cewa shi Bahaushe ne.

A irin wannan lokaci na bukin Ranar Hausa ne ya kamata mu yi nazari a kan wasu muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar Bahaushe, al’adunsa da ɗabi’unsa. Domin duba ta yaya za a inganta su? Yaya Bahaushe a wannan zamani zai dawo da kima da martabarsa a idon sauran ƙabilu da harsuna masu tarin yawa da ake da su a qasar nan, da duniya baki ɗaya?

Abin takaici ne da mamaki yadda rayuwar ’ya’yan Hausawa ta zama wani abu daban, savanin yadda a baya muka taso cikin kyawawan al’adun gargajiya da tarbiyyar addinin Musulunci da muke taƙama da su. Amma yanzu wannan duk ya canja, an koma kwaikwayon wasu baƙin al’adu da watsi da tarbiyyar mu ta asali. Matasanmu sun koma rayuwa irin ta ƙabilu ko turawa kamar yadda suke gani a finafinan ƙetare da shafukan sada zumunta. Sun koma sanya kayan da suka sava da tsarin al’adunmu da tarbiyyar addininmu.

Idan ka ga ’yar Bahaushe cikin sakakkun kaya masu rufe surar jiki da kamala a tare da ita to, mai yiwuwa an yi rasuwa ne ko za ta je Islamiyya ko kuma tsari da sa ido na gidan da ta fito ya takurata ta yadda tilas ta fita a haka. Amma kuwa a mafi yawan lokuta kayan da ke jikinta matsattsu ne, masu nuna siffar jikinta, wani lokaci ma babu ko lulluɓi tare da ita.

Haka su ma mazan in ba a ɗaurin aure ko wata rasuwa ta jiki ko taron mauludi da bukin Sallah ba, da wuya ka ganshi cikin doguwar riga ko babbar riga. Saboda suna ganin tsofaffin al’adu ne, na gargajiya da ba sa nuna wayewa a tare da su.

Haka idan an zo batun magana ko rubutu da harshen Hausa, za ka ji kamar ka yi kuka jin yadda ake magana da wata irin bagwariyar Hausa ko ingausa, a ɗauko Turanci a gwama da Hausa, wasu kalmomin ma sai ka rasa ma’anar su a Hausa, amma su suna gani wai shi ne daidai, kuma wasu har da iyaye ko manyan da ya kamata sun tsawatar ko su yi gyara a maganar, amma sai dai kawai su yi dariya a kawar da kai.

Haka ma a wajen rubutun Hausa, da dama daga cikin matasan mu ba su san yadda ake rubuta akasarin kalmomin Hausa ba, sai dai su ƙirƙiro wani irin abu bisa tunanin haka ya kamata ya zama. Idan ka ga yadda ake rubuta kalmomi irin su ’yar, tsa, qya, za ka sha dariya, saboda kwata-kwata ba su ɗauki hanya ba. Ko da yake wani lokaci ba za ka ga laifin su ba, saboda ba a koya musu a gida ko a makaranta ba, saboda rashin mayar da hankalin iyayen wajen koyawa yaransu muhimmancin sanin al’adun su, harshen su, da ƙa’idojin rubutun sa.

Haka ma a makarantu, ba duk makaranta ce yanzu za ka tarar akwai malamin koyar da Hausa ba, ballantana sauran harsuna. Sai an zo jarabawar kammala babbar sakandire ka ji ana cewa, yara su ɗauki darasin Hausa don su ƙara yawan sakamakon da suka samu, domin ana ganin shi ne darasi mai sauƙi. Amma ko shi ma ɗin da za a ba ka damar duba, takardun jarabawar da aka rubuta, sai ka ji kamar ka yi kuka.

A yayin wani bincike da na gudanar kan yadda ƙananan makarantu na firamare da ƙaramar sakandire ke koyawa yara ilimi da harsunan su na gado, kamar yadda dokar ilimi ta ƙasa ta ba da dama. Abin da wata Darakta a Hukumar Kula da Ilimi ta Bai Ɗaya ta sanar da ni shi ne, su kansu malaman ba su gama sanin harshen nasu ba, ballantana su koyawa wani!

Don haka wannan batun ma babu shi, ana koyarwa da turanci ne yadda za a gane kawai. Kuma hakan ne, domin kuwa in ba a ƙauyuka ba inda ake tasowa cikin al’adar amfani da harshen uwa ko harshen gado a kowacce sabga ta rayuwa, idan a birni ne ba ya yiwuwa.

Abin mamaki ne hatta a wasu gidajen watsa labarai da jaridu inda suke zama kamar makarantun koyar da harshe, za ka riƙa ji ana amfani da wata irin Hausa, ko kuma yadda ake rubuta wasu kalmomi ba a yadda suka dace ba. Saboda yadda ake ganin duk abin da ka faɗa in dai za a gane kawai daidai ne, ba lallai sai ka san ƙa’idojin amfani da su ba. Kuma wannan irin halayya ta nuna ko-in-kula da harshen gado, shi ne yake kai mu ga irin haka, ta yadda ingancin harshen ke ƙara komawa baya.

Ko da yadda wasu matasan marubuta adabi da suke ƙoƙarin nuna basirar su a harkar rubuce-rubucen Hausa, za ka tarar rubutun kawai ake zubawa ratata, babu tsari ko kiyaye ƙa’idojin rubutu. Kuma yayin da ake samun wasu ƙalilan da ke ƙoƙarin sanin haruffan Hausa da ƙa’idojinsu, wasu kuwa ko oho, suna ganin in dai wasu za su gane abin da suke rubutawa to, su babu wani abu da wani zai koya musu.

Shi ya sa ko kana son karanta wani labari da suka yi, sai kan ka ya kulle ka kasa karatun. Sun kasa gane cewa, duk abin da ake so a yi shi da kyau sai an koye shi, ko da kuwa cin abinci ne, yana da ladubbansa.

Idan ka shiga wasu gidajen ‘yan boko na ƙasar Hausa ba kasafai za ka ji ana magana da harshen Hausa ba, ballantana ka ga an sayo littafi ko jaridar Hausa ana karantawa, don nishaɗi da qarin ilimi ba. Shi ya sa marubutan mu kullum a wani irin yanayi, saboda ba a damu da sayen littattafan da suke rubutawa ba, jaridunmu na Hausa kullum sai mutuwa suke yi, saboda ba a saya, musamman matasa, sai dai dattijai ko ‘yan kasuwa, waɗanda su ma akasari karatun nasu bai wuce na yaƙi da jahilci ba, amma saboda kishi da son sanin halin da ƙasa ke ciki suke jajircewa wajen saye kowanne mako.

Lallai ya kamata masana da manazarta harshen Hausa su ba da himma wajen faɗakar da iyaye da sauran jama’a masu raino da haƙƙin koyarwa, su ɗauki batun koyawa yara masu tasowa yin amfani da kalmomin da suka dace na asalin Hausa da kuma koya musu ƙa’idojin rubutun Hausa yadda ya dace, don su girma da sanin muhimmancin sa a rayuwarsu, da sa musu kishin harshen don su zama masu alfahari da shi a ko’ina. A maimakon karaɗe zaurukan sada zumunta kamar yadda aka saba kowacce shekara, ana gasar rubuta kalmomin Hausa ko karin magana.

A riƙa shirya taruka tsakanin ƙungiyoyi, ana tara malamai, manazarta da ‘yan jaridu, domin tattauna batutuwa da ƙalubalen da suka shafi rayuwar Hausawa da harshen Hausa, da kuma yadda harshen ko al’ummarsa za su kawo wa duniya canji da cigaba. Shirya raye rayen gargajiya, bayyana sutura da girke-girken al’adun gargajiya na Hausawa da baje kolin rubuce-rubucen tarihi da nishaɗantarwa da masana ilimin harshe suke samar wa.

Sannan a riqa zurfafa bincike wajen fitar da take ko darasi da za a mayar da hankali a kansa wajen bukin wannan rana, don ya dace da yanayi ko lokacin da ake ciki, da nufin duba irin gudunmawar da Bahaushe ke bayarwa a wannan ɓangaren.

A yayin da nake yabawa da gudunmawar da waɗanda suka jajirce wajen raya bukin wannan rana irin su Malam Abdulbaqi Jari, ma’aikacin BBC Hausa, wanda aka ce shi ya fara bai wa wannan rana muhimmanci a harkokin da yake yi a zaurukan sada zumunta, manyan masana harshen Hausa, irin su Farfesa Ibrahim Malumfashi, Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau da sauran fitattun manazarta bisa gudunmawar da suke bayarwa a kowanne lokaci don ganin harshen Hausa ya samu havaka da samun karɓuwa a duniya.

Domin ayyukan su ne suka sa har aka kawo wannan lokaci, da bukin Ranar Hausa ta Duniya ke daɗa samun karvuwa a tsakanin matasa da sauran jama’a, har ma da waɗanda ba Hausawa ba, inda suke ƙara nuna sha’awarsu ga nazarin harshen Hausa, wanda shi ne harshe na goma sha ɗaya da aka fi amfani da shi a duniya.

Kafin in kammala sai na jinjinawa, Malam Auwal Janyau, ma’aikaci a Sashin Hausa na BBC, wanda ya ƙirƙiro wata hanya ta ilimantar da Hausawa da masu son koyon rubutun Hausa, yadda ya dace a riƙa rubuta kalmomin Hausa, a shafukansa da ke zaurukan sada zumunta. Abin da ya kawo gagarumin cigaba wajen inganta yadda matasanmu musamman marubuta ke gudanar da rubutunsu cikin harshen Hausa.

Babu shakka irin wannan gudunmawa harshen Hausa ke buƙata daga masana, manazarta da ’yan boko da ke gadara da harshen, domin ’yan baya su taso da sanin martabar harshensu na gado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *