Sheikh Giro Argungu ya riga mu gidan gaskiya

Allah Ya yi wa fitaccen malamin Islam na ƙungiyar JIBWIS, Sheikh Abubakar Giro Argungu, rasuwa.

A ranar Laraba Allah Ya yi masa cikawa a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi bayan fama da rashin lafiya.

Marigayin ya bar duniya yana da shekara 68.

Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya ba da sanarwar marigayin a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.

A na sa ran gabatar da jana’izar marigayin a wannan Alhamis kamar yadda Sheikh Bala Lau ya sanar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *