Kotu ta kori ƙarar su Atiku kan Tinubu

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe mai zamanta a Abuja ta kori ƙarar da Jam’iyyar PDP da ɗan takararta na shugabancin ƙasa, Atiku Abubakar suka shigar inda suke ƙalubalantar nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu a babban zaɓen da ya gabata.

Kotu ta yi watsi da ƙarar ne a zaman shari’a da ta yi ranar Laraba.

Yayin zamanta, kotun ta soke wasu sakin layi a ƙorafin da aka shigar da suke nuni da Shugaba Bola Tinubu bai cancanci shiga zaɓen da ya gudana ranar 25 ga Fabrairun da ya gabata ba.

Ta ce masu ƙarar sun gagara gabatar wa kotun cancantar da ta dace a same ta kafin shiga zaɓen.

Kazalika, Kotun ta soke wasu sassan ƙarar inda aka zargi Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi da wani mai suna Friday Adejo (wanda aka bayyana a matsayin shugaban wata ƙaramar hukuma a jihar Kogi).