Mun yaba da ayyukan gwamnatin Jihar Kano na cigaban al’umma – Danpass

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Dan Saran Kano Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass, basarake, ɗan kasuwa kuma fitaccen ɗan siyasa, ya yaba da irin ayyukan da gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf take wajen bunƙasa cigaban al’umma.

Ya ce zuwan Gwamnatin Abba ta ɗauki matakai na ganin an kyautata harkar ilimi ta gyaran makarantu da samar da kayan aiki da kyautatawa malaman da suke koyarwa domin su samu kyakkyawan yanayi na koyar da ɗalibai.

Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ya kuma yaba da yanda Gwamnatin Abba take gudanar da tsarin ciyarwa Azumi da ake domin kuwa abinci mai kyau da ake ciyar da ɗinbin mutane a lokacin shan ruwa da hatta ‘yan adawa sun yaba da yadda ake rabon abincin.

Ya ce su dama suna da kyakkyawan zato na alkhairi ga Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf wacce ta zo ta samu jihar a wani yanayi da gwamnatin baya da muƙarrabanta da  suka tafi suka bar abubuwa a damalmale sai yanzu ake ta ƙarin kawo gyara.

Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass, ɗansaran Kano ya ƙara jaddada kiransa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwamishinan kasuwanci Shehu Wada Sagagi akan samar da wadattaccen wuta a jihar Kano da za su taimaka wajen farfaɗo da ɗimbin kamfanoni da suka mutu manya da ƙanana.

By ukarofi