Muna da burin shirya musabaƙar Alƙur’ani na bebaye, kurame da makafi a Jami’ar Khairun – Farfesa Garba 

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Jami’ar Khalifa Isyaka Rabiu an samar da ita ne bisa tunanin Khalifan Tijjaniyya marigayi Sheik  Isyaka Rabiu ne,wanda shine ya ƙirƙiro ta ta  zama kuma cikamakin ayyukan alkhairi da yake yi  kamar yanda aka san shi a yaɗa karatun ƙur’ani da haddar sa da gina masallatai da masallatan ta kyautatawa limamai da sauran abubuwa,haka ma ya yiwa karatun zamani hidima ta kafa makarantar furamare,da ƙaramar sakandire da babba  sai kuma ya ƙirƙiri wannan  jami’a.

Mataimakin shugaban Jami’ar Khairun, Farfesa Abdulrashid Garba ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida ya ce Allah cikin ikonSa  bai nufa  Khalifa zai  ga jami’ar da ya assa  ta soma gudanarwa yana raye ba amma sai Allah ya wadata shi da ya’ya nagartattu  nagari suka zo suka ɗauki lamarin tafiyar da ita suka samar mata lasisi daga Gwamnatin Tarayya aka kafa duk abubuwa na shugabanci kama daga kwamitin amintattu ƙarƙashin Emiratos Farfesa  Sani Zahraddeen da kwamitin zartarwa ƙarƙashin Farfesa Isyaku da na gudanarwa a ƙarƙashin shugabancinsa.

Ya ce da suka zo jami’ar a cikin watan hucu na  Agusta shekarar 2024 suka yi ta ƙoƙarin suga karatu ya kankama suka cigaba da zaƙulo mutane da za su zo ,su riƙe musu tsangayoyin su na ilimi suka ɗauki ɗalibai bayan sun je Abuja sun gama ganin duk wanda yakamata akan a basu amincewa za su ɗebi ɗalibai suka zo suka ɗibi ɗalibai suka fara karatu a watan biyu na 2024 sannan suka samar da majalisar Dattawa ta jami’ar wacce ita ce ruhin jami’a.

Farfesa Abdulrashid Garba ya ce sun samar  da duk abinda ake buƙata na jami’a suka fara karatu Allah ya na basu nasarori yanzu har sun gama shekarar Ilimi ta farko, yanzu sun shiga na biyu sun ɗebi daliban farko guda 100 yanzu sun ɗebi na biyu wajen  700 su na nan sun fara karatu.

Ya ce a cikin irin hikima ta Khalifa sheik Isyaka Rabiu sai ya yi niyyar ya kafa jami’a don ya samar da masana a guraben da babu su a Kano da yawa  sai yaga abinda yafi dacewa a karkata akala akan abinda ya shafi kimiyya da fasaha, ya amince a fara da harkokin kula da lafiya a ɓangarori daban daban akayi tsangaya na ɗaya mai darussa uku  na biyu  na fasaha mai  darussa uku sai tsangayar kimiyya da computa da yake da darussa 10  a yanzu dai jami’ar na da tsangayoyi uku darussa 16 kowanne kuma na da shugaban sashe wanda Farfesa ne ko wanda ya kusa zama Farfesa ke kula da shi.

Ya ce dama duk shugabannin tsangayoyi farfesoshi ne, kuma sun ma fara yunƙuri na kafa tsangayar Shari’ar Musulunci har sun ɗauki shehin malamin da zai assasa musu da zarar an fara shekarar  karatun 2025  za su buɗe a   fara neman ɗaukar masu karatun lauya jami’ar za ta zama tana da tsangayu guda huɗu da darussa 17 ƙari kan darussan guda 16 da suke.

Ya ƙara da cewa dukkan tsangayoyinsu  na kimiyya da fasaha ne zunzurutu sai kuma na sharia da suke ƙoƙarin sawa shi ma saboda shari’ar Musulunci suke so su yi domin wasu sai su je waje suyi karatun shari’ar Musulunci, amma sai su zo ƙasar nan a hana su shiga  kotu, wannan ba abu ne mai daɗi ba, shi ya sa suke so suyi ta yadda za a bar su su shiga kotu ko a matsayin Alƙalai ko lauyoyi.

Ya ce jami’ar ta Khairun ta yi duba da tarbiyya na gidan Khalifa na ƙur’ani da kasuwanci sai suka shigo da tsari a  jami’ar ko me kazo karantawa cikin darussa 16 lallai duk mako sai ka yi karatun Al’ƙur’ani kuma suna bibiya idan baka yi ba, idan aka zo wani zangon karatu sai ka nanata kuma za a baiwa kowanne shaida na darasi da ya yi na ƙur’ani sanan sun kuma gina wajen koyar da sana’oi da za a riƙa koyawa ɗalibai  sana’o’i zai zamana duk wanda ya gama jami’ar zai fito ya iya dogara da kansa.

Ya ce wani bambancinsu da sauran jami’oi shine duk ilimi idan babu tarbiyya bai cika  ba , shi yasa duk ɗalibin  da ya shigo jami’ar sai an ƙarfafa shi akan tarbiyya in ka sami ilimi ka iya mu’amala da Ubangiji ta jin tsoron sa  da girmama  iyaye da jama’a da  abokai da kyautatawa tsakanin mace da mijinta da duk kyawawan dabi’u  abinda suke koya musu kenan a ɓangaren  tarbiyya shi ya sa digiri da suke bayarwa ya bambanta da sauran.

Mataimakin Shugaban Jami’ar na Khairun, Farfesa Abdulrashid Garba ya ce a  lokacin da Gwamnatin tarayya ta bada izinin a gina jami’ar sai kuma ta sahale a zo a gina cibiyar ƙasa da ƙasa na nazarin kimiyyar Al’ƙur’ani da yanzu take ƙarƙashin kulawar Barista ɗan’almajiri  sai ta fara da tattaro Alarammomi 88 aka yi ganawa dasu saboda suna so su haɗu dasu su mori darajar ƙur’ani da Allah ya basu su kuma su mori zamananci da za su bijiro musu da shi.

Ban da wannan sun kira wata yarinya da ta yi na ɗaya a musabaƙar ƙur’ani na duniya ta zo jami’ar sun karramata. Cibiyar tana da muhimman shirye shirye guda huɗu da zata gudanar  na farko tana so tayi musabakar ƙur’ani na Bebaye na biyu na Kurame na uku tana so tayi taron Alarammomi mata sannan tana so tayi musabaƙar rubutun Al’ƙur’ni banbancin su da wanda ake karantawa idan an zo ba karatun za a yi ba, in an karanto maka rubutawa zaka yi kamar yanda ake satu. Alarammomi gwanaye ne zasu zo su duba suyi alkalanci . 

Daga cikin tsare-tsaren da suke dashi a jami’ar wajibi ne ma’aikatan su  sai sun yi karatun ƙur’ani ana koyar da karatun ga ma’aikatan sau ɗaya a mako akwai malama da take koyawa  mata da malami na ajin maza da ake koyawa ma’aikatan ƙur’ani.

Farfesa Abdulrashid Garba ya ce jami’ar ana gudanar da ita ne ba don riba ba, shi ya sa kuɗin makarantar ya zama mafi sauƙi fiye da   dukkan jami’o’i da suke kwasa kwasai irin nasu a ƙasar nan sannan bayan an gama lissafin biyan kudin makarantar.

Abdulsalam Isyaka Rabiu ya yi ragi ga ɗaliban farko  sannan ya ɗauki nauyin mutum 500 za suyi karatu kyauta sannan babu abinda ake buƙata na kayan aiki  akwai ɗakin gwaje-gwaje  dana   karatu dana harkar yanar sadarwa akwai  duk  wani abu na koyo da koyarwa na zamani .ɗakin kwanan ɗalibai guda Bakwai ne na maza dana mata kuma tsarin ɗakunan nasu irin  yanda ake a makarantun Sakandire ne basu  yarda da ware ɗaki ga dalibai ba, akwai lokacin shiga dana  fita dana  kashe wutar lantarki dana kunnawa   da lokacin shiga dana fita daga makwanci dan haka ma  kafin iyaye su kawo ya’yansu suna  sanar da sharuɗɗan jami’ar in sun yarda da sharuɗɗan su su kawo ya’yansu  shi yasa ba sa saka kuɗi da yawa.

Farfesa Abdulrashid Garba  ya yi fatan Allah yasa jagorancin da suke a  jami’ar  ta Khairun  yanda aka ba su amana suka karɓa da yardar Allah za su riƙe amanar bisa gaskiya da adalci.

By ukarofi