Yanzu ake buƙatar haɗin kan al’umma da gwamnati domin farfaɗo da harkar ilimi – Hamisu Rabiu

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana cewa taron tsofaffin ɗalibai da ake wani dandali ne na sada zumunci taron da ‘yan makarantar ɗandago suka yi mai albarka ne da tarihi da ba a taɓa irin sa saboda sun ga kakanni da iyaye da yayye da ƙanne, an zo an ga fuskokin juna ko haka kaɗai aka yi aka tashi an yi zumunci.

ɗaya daga cikin tsofaffin ɗaliban makarantar ‘yan aji na 87 kuma fitaccen ɗan kasuwa shugaban Hamir Global ɓenture Alhaji Hamisu Rabiu ne ya bayyana hakan a yayin taron cikar makarantar firamare na ɗandago shekaru 90 da kafuwa da aka gudanar a makarantar.

 Ya ce ga shi kuma ana tattauna matsalolin makarantar abinda ya shafi ajujuwa da ban ɗakuna da malamai da komai don a inganta ta ko ba komai wani taro ne na alkhairi kuma taro ne me albarka da suke farin ciki da shi.

Hamisu Rabiu ya ce duk inda suka taka a rayuwa suna kallon baya suna kallon makarantar tamkar ita ce uwa ita ce uba kuma abinda ya kawo mutane taron kishi ne  da irin wannan haɗuwa za ka ga irin cigaba da makarantar za ta samu.

Don haka ya yi kira ga tsaffin ɗalibai kowanne su riƙa haɗuwa suna kafa ƙungiya kamar yadda suma suka kafa ta 1987 ya zama suna haɗuwa ko sau biyu a shekara su zo su zagaya makaranta aƙalla za su ga matsala da za su iya sa hannu su taimaka, domin sai an haɗu wani zai kawo tunani wani kuma Allah ya bashi hali wani lokaci da zai sadaukar.

Ya ce kamar wasu ayyuka da suke a makarantar wasu haɗaka aka yi shi da Allah ya sa zai bada dukiya wani ya bada lokacinsa wani shawara shi yasa aikin da suke a makarantar na gine-gine ya yi nasara don haka tsaffin ɗalibai suyi amfani da damar su domin cigabantar da makarantunsu.

Alhaji Hamisu Rabiu ya ce a lokacin da suke a makarantar ɗandago furamare basu da yawa a aji basa wuce su 30,40 amma yanzu aji ɗaya sai a sami ɗalibai sama da 100 sannan da akan kujeru da bencina suke amma yanzu saboda yawa yanzu ba maganar abin zama ba daidai da daɓe da yara zasu zauna  babu  shi a wasu ajujuwan, saboda haka yanzu ake buƙatar haɗin kai da gwamnati domin fitar da harkar ilimi daga halin da yake ciki.

By ukarofi