Muna farin ciki da digirin girmamawa da Jami’ar North West ta ba Marigayi Ɗantata  – Mustapha AJ

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Sakataren Maragayi Alhaji Aminu Ɗantata, Alhaji Mustapha Abdullahi Junaidu ya bayyana cewa su da suka kasance tare a lokacin rayuwar Maragayi shi da iyalan sa da masoyansa sun kasance suna farin ciki da wannan digirin girmamawa da Jami’ar Norhwest NWU ta bashi bayan rasuwarsa bata fasa cika alƙawarin da ta yi ba na ba shi wannan digirin tun yana raye. Ya ce wannan kyautatawa da wannan jami”a ta yi ya sake sabunta musu alhinin rashin sa da kuma farin ciki na cewa alkairinsa da mu’amalarsa da kuma yabon da wannan jami’a da sauran al’umma suke yi masa to ya samu farin ciki da kuma yin alhini a lokaci guda.

Alhaji Mustapha Abdullahi Junaidu ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai bayan miƙa kyautar digirin girmamawa da Jami’ar Northwest NWU ƙarƙashin shugabancin Farfesa Abubakar Kurawa ta yi a ranar Asabar ɗin nan da ta gabata a harabar jami’ar na dindin da ke birnin Kano.  

Haka kuma Alhaji Mustapha AJ ya ce matsayin sa na sakataren Maragayi  wanda ya samu zama da shi na tsawan lokaci akwai darussa masu yawa da ya gani wanda sai an haɗa jami’o’i da yawa za a iya samun darasi da yake so su ma su koya da sauran al’umma domin alfanun abubuwan da ya gani daga rayuwar maragayi, yace darussan na da yawa sosai amma kaɗan daga ciki da zai faɗa a wannan lokaci shi ne na farko duniya dai Allah ya bai wa ɗantata, amma abun mamaki shi ne kuma ya juya mata baya ta yadda kullum za ka ji burinsa shi ne kyautatawa ɗan adam wanda babu wani abu dana ga Maragayi ya ba muhimmanci sama da wannan a iya sanina sai kuma abu na biyu shi ne cika alƙawari idan ya yi alƙawarin cewa zai baka naira kaza to fa kafin ranar ta zo ya soma tambaya yaushe ne muka yi alƙawarin wane zai zo lokacin ya yi? in bai yi ba sai in ce masa lokaci kaza ne in ma ya yi nan ma sai na gayamasa bayan mun gama a wannan lokaci sai y ace wacce maganar ce kuma a gaba ? ida wata maganar sai ince kaza ne in kuma babu wata sai ince iya dai sanina wannan ce sai in shiru sai ince sai dai kuma inda wata daga gareka haka dai akayi  ta yi ba gajiyawa a wannan yidima ake, shi ne muke cewa Allah yasa muyi rayuwa irin ta Ciyaman.

A ƙarshen Alhaji Mustapha Abdullahi Junaidu ya ace ba shakka mun koyi darusa mai yawa kuma abubuwa na alkairi kamar yadda iyalan sa suke masa biyayya suke ƙaunarsa yake ƙaunar su da kuma irin tarbiyya da biyayyar da suke masa abubuwa na alkairi za su cigaba ba da daɗewa ba da ikon Allah sai kuma yadda ya rayu a duniya cikin ƙaunar addini da jindadi yiwa addini hidima to muna kyautata zaton canma yana cikin niimar ubangiji da ikon Allah, NWU ta yi bikin yaye ɗalibai a ƙaron na biyu wanda ta bada digirin girmamawa ga wasu fitattun mutane da suka yiwa ilimi da alumma hidima ciki kuwa harda tsohon gwamnan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya kafa jamioi biyu a Kano wanda suka haɗa da ADUSTECH Wudil da kuma NWU Kano a zamanin da yake gwamnan Kano wanda wani ɗalibi Aminu Aminu Madugu ya ce yana daga cikin wanda ya ci gajiyar kafa waɗannan jami’o’i biyu a Kano. 

By ukarofi