Muna fatan samun haɗin kan jama’a wajen tattara sakamakon zaɓe a Kano – INEC

Daga RABIU SANUSI a Kano

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta buƙaci haɗin kan masu ruwa da tsaki a Jihar Kano yayin tattara sakamakon zaɓe da yafara gudana a jihar kano.

Kiran ya fito ne daga bakin shugaban kwamitin tattara sakamakon zaɓe na hukumar zaɓe na jihar Kano, Farfesa Lawal Suleiman Bilbis.

Tuni dai hukumar zaɓen ta jihar Kano ta fara tattara sakamakon zaɓen daga ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar.

Fargesa Bilbis shi ne shugaban tattara sakamakon zaɓe a hukumar zaɓe ta jihar Kano.