Atiku ya buƙaci jami’an tattara sakamakon zaɓe su dinga shigarwa tun daga rumfuna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu da ya umurci jami’an tattara sakamakon zaɓen na ranar Asabar da su dinga shigar da sakamakon zaɓe tun daga rumfunan zaɓe.

A cikin sanarwar da mai bai wa Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mista Paul Ibe ya sanya wa hannu, ya ce kiran ya zama wajibi “a binciki wasu gwamnonin da ke ƙoƙarin yin maguɗin zaɓe a matakin ƙananan hukumomi,” inji shi