Atiku zai lashe zaɓen Shugaban Ƙasa, cewar Gwamna Bala

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ya bayyana cewar, yana da yaƙin ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar su ta PDP, Atiku Abubakar zai lashe kujerar shugabancin Najeriya.

Inji gwamna, “A yanzu dai ba zance komai ba, amma muna jaddada tsammani ɗan takarar mu na shugaban ƙasa, Wazirin Adamawa zai ci zaɓen nan da ikon Allah, da kuma sauran ‘yan takarkari na sanatoci da ‘yan majalisar tarayya.

Sanata Bala Mohammed wanda yayi wannan furuci a mazabar sa ta Bakin Dutse dake garin Yelwan Duguri ta jihar Bauchi, ya kuma nuna gamsuwar sa da yadda na’urar zaɓe ta BVAS ke aikatuwa.

“Kamar yadda nace kimiyyar na’urar zaɓe, wato BVAS, da zuwa na bada ɓata wani ba aka sanya yatsuna akan na’urar, da kuma aka ɗauki hotona sai komai ya fito daidai a fili, kuma aka bani takardar ƙuri’a na kaɗawa na kaɗa”.

Gwamnan wanda ya yi hasashen nasara da zaman lafiyar ƙasar nan, ya kuma nuna gamsuwa sa da yadda hukumar zaɓe take gudanar da zaɓuɓɓuka na ‘yan takarkaru na madafun mulki daban-daban.

Ya koli matasa da mata dasu cigaba da yin juriya da haƙuri domin dimokradiyya ta cigaba da zama da gindin ta, kana jama’a su mori amfanin ta.

Gwamna Bala ya lura da cewar, ga dukkan alamu, za’a gudanar da dukkan zaɓuɓɓuka na madafun mulki dabam-dabam cikin kwanciyar hankali da kyakkyawan zamantake wa.

A wani cigaban kuma, tsohon mamakin majalisar tarayyar Najeriya, Yakubu Dogara ya nuna takaicin sa dangane da na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS data kasa ta zance shi a tsawon lokaci ana taba.

Yace, “Kuma musamman duk tashar yin zaɓe data kasance akwai masu kaɗa kuri’a kimanin dubu biyu (2, 000) kamata yayi a basu na’urar BVAS guda huɗu.

Dogara, wanda yake yiwa manema labarai jawabi a mazaɓar sa ta Gwarangah mai lamba 007 dake cikin ƙaramar hukumar Bogoro ta jihar Bauchi, yace ɗaya daga cikin BVAS guda biyu da aka samar wa maganar tasu, guda ɗaya ba ta aiki.

Da yake nuna damuwar sa bisa aka yi da ake samu dangane da na’urar ta BVAS INEC, Dogara yace “Masu jefa ƙuri’a sun kai kusan dubu biyu a maganar mu, kamata ya yi a bamu BVAS guda huɗu, amma sun kawo biyu, kuma cikin biyun ma, guda baya aiki”.

“Muna ganin wannan aniya ana nema ne a lular da mutane ne idan sun fito su yi fushi, su koma gida suke ba zasu yi zaɓe ba, to amma ana takan bayar da haƙuri dai, kowa zai iya gani a nan irin abubuwa da suke faruwa”.

Dogara ya bayyana cewar, tunda sun fito da niyyar kaɗa ƙuri’un su, zamu jira muga gudun ruwan jami’in zaɓe (EO), idan BVAS ɗin ya lalace ba zai yi aiki ba, tilas su haƙura su koma gidajen su”.

Domin kamar yadda Dogara yace, Allah ya sani muna da niyyar kaɗa ƙuri’ummu, suma sun sani, kuma kuma manema labarai kun shaida cewar, muna da niyyar kaɗa kuri’ummu, amma INEC sun hana mu”.

Tsohon kakakin majalisar sai ya yi roƙon idan an sanar da sakamakon zaɓuɓɓuka, kada jama’a su tayar da tarzoma domin, kamar yadda ya ce, “Munana bukatar zama lafiya domin mu gina ƙasar mu, kowa yayi haƙuri a zauna lafiya domin a siyasa wani yaci ne wani ya fadi, babu inda aka tava yin zaɓe aka ce dukkan ‘yan takara sun ci zaɓe”.

Misali, kamar yadda sakamakon zaɓen yake nuna wa, jam’iyyar PDP ta lashe a mazavar Gwamna Bala Mohammed ta Bakin Dutse dake Yelwan Duguri kamar yadda sakamakon ke nunawa a ƙasa

Zaɓen shugaban ƙasa:

PDP= 103
APC= 25

Majalisar wakilai ta tarayya:

PDP =82
APC= 65
NNPP 5 ADP 1
LDP_ 1

Sanata

PDP =101
APC =32
NNPP =17

Makarantar firamare ta Yelwan Duguri

Shugaban Ƙasa_

PDP= 103
APC= 25

Majalisar Wakilai

PDP =82
APC= 65
NNP 5 ADP 1
LDP – 1
Bandaron kuri’a -1

Sanata

PDP =101
APC =32
NNPP =17