Muna gamsuwa da jagorancin gwamnatin Katsina – Hamisu Ɗanja

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Mataimakin shugaban ƙungiyar masu gudanar da harkokin kasuwancin gwari ta ƙasa, Alhaji Hamisu Malam ɗanja, ya bayyana cewar shi da sauran al’ummar jihar Katsina da kewayenta gabaɗaya suna cigaba da gamsuwa da jagorancin Gwamnan Jihar katsina Dakta Alhaji Dikko Umar Raɗɗa a Katsina.

Mataimakin shugaban ƙungiyar ta ‘yan gwari na ƙasa Alhaji Hamisu Malam ɗanja ya yi wannan tsokacin ne a ɗanja a lokacin da yake zantawa da Jaridar Blueprint Manhaja dangane da wannan al’amari, inda ya cigaba da cewa haƙiƙa Gwamnan jihar ta Katsina Dakta Alhaji Dikko Umar Raɗɗa mutum ne mai tausayin talakawan jihar Katsina idan aka yi la’akari da irin yanda yake kawo sauyi da kuma ayyukan cigaban jihar Katsina tare da kawo bubuwan jin daɗin more rayuwar al l’ummar baki ɗaya.

Ya ce ko a kwanan nan ma ya raba wa al’ummar jihar Katsina kayayyakin gudanar da sana’o’i da waɗanda suka jiɓanci injinan ban ruwan kayan gwari da injinan yin walda da markaɗe da kayan abinci waɗanda suka jiɓanci shikafa, taliya da sauransu.

Hamisu Malam ɗanja ya ƙara da cewa bisa ga irin wannan taimakon da yake yi wa al’ummar jihar Katsina ne yake ganin ya kamata ya ƙara roƙon mai girma Gwamnan Dakta Alhaji Dikko Umar Raɗɗa da ya ƙara ƙoƙari wajen kammala madatsar ruwa dake garin ɗanja domin manoman gwarin jihar Katsina su cigaba da amfana, sannan kuma ya taimaka ya yi masu odar kyakkyawan maganin tsutsar nan mai suna Ibola mai lalata masu tumatiri a wajen noman sa.

Ya ci gaba da bayyana irin cigaban da kasuwancin gwari yake samu daga shekaru kaɗan baya da suka gabata zuwa yanzu, ya ce haƙiƙa daga wancan lokacin zuwa yanzu kasuwancin gwari ya samu cigaba, a cewarsa cigaban da kasuwancin gwarin ya fara samu shine a wancan lokacin suna yin zubin tumatiri ne a kwanduna zuwa kasuwannin da suke saidawa, amma yanzu an samu cigaba suna zubawa ne a kiret din roba zuwa kasuwannin da suke saidawa kuma suna samun sauƙin ruɓewar kaya akan hanyarsa ta zuwa kasuwa.

By ukarofi