Murar Tsuntsaye: An yi kira ga al’ummar Kano su kwantar da hankula

Daga BELLO A. BABAJI

Yayin da al’umma ke cigaba da fargabar yaɗuwar cutar murar tsuntsaye da ake kira ‘avian influenza’ a Kano, Gwamnatin jihar ta yi kira ga al’umma da su kwantar da hankulansu tare da ruwaito duk wani abin zargi da suka gani ga hukumar da ta dace.

An samu rahoton ɓullar cutar ne a watan Disambar 2024 bayan wani mutum daga Ƙaramar Hukumar Gwale ya sayo wata agwagwa daga kasuwar Janguza inda ya kai ta cikin gidan kiwon kajinsa, wanda daga bisani suka fara nuna alamun rashin iya yin numfashi yadda ya kamata. Daga nan sai guda 35 cikin 50 suka mutu.

Bayan zuwa asibitin dabbobi dake Gwale ne sai aka tabbatar da ɓullar cutar.

Nan da nan sai Ma’aikatar Gona ta jihar ta sanya jami’anta yi wa wajen feshi tare da rufe shi, sannan kuma suka je wajen sayar da kaji na Janguza da wayar da kan al’umma game da cutar.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran Ma’aikatar Lafiya, Ibrahim Abdullahi ya fitar, Kwamishinan Ma’aikatar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya yi kira ga al’umma da su kwantar da hankula, ya na mai cewa lamarin bai yi girman da za a sanar da ɓarkewarsa ba.

Ya ce la’akari da shafar mutane da cutar kan yi, sun tattauna da tawagar bada agajin gaggawa da kwamitocin lafiya da Ma’aikatun Gona da na Ruwa don magance matsalar.

Kwamishinan ya kuma bayyana alamomin cutar, waɗanda suka haɗa da zazzaɓi, majina, da idanu su yi jazir da sauransu, ya na mai kira ga al’umma musamman masu kiwon kaji da su kula sosai tare da aiko da rahoton duk wani rashin lafiya da suka gani a tsuntsayensu ga hukumomin da suka dace don ɗaukar mataki akan lokaci.