Aƙalla mutane 14 da ake zargin masu hakar ma’adinai ne ba bisa ka’ida ba sun mutu, yayin da wasu takwas suka jikkata bayan wani tsohon wurin hakar ma’adinai ya rushe a Afirka ta Kudu.
Lamarin ya faru ne a daren Litinin a kusa da Rustenburg, da ke lardin North West na ƙasar, a lokacin da mutanen ke aikin neman wasu karafa daga cikin tarkacen wani tsohon wurin hakar ma’adinai.
Kwamishinan ’yan sandan lardin, Arthur Peter Adams, ya ce har yanzu ba a san adadin mutanen da ka iya kasancewa a ƙarƙashin tarkacen ba.
Ya ce jami’an ceto na ci gaba da bincike domin gano ko akwai wasu da suka maƙale a wurin.
Daga cikin waɗanda suka jikkata akwai ’yan ƙasar Lesotho, yayin da har yanzu ba a tabbatar da ƙasashen da waɗanda suka mutu suka fito ba.
Haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ta dade tana addabar Afirka ta Kudu, inda mutane ke shiga tsoffin wuraren hakar ma’adinai domin neman sauran ma’adinan da suka rage.
Wasu daga cikin waɗannan ayyuka na faruwa ne a ƙarƙashin ƙungiyoyin masu aikata laifuka, waɗanda a wasu lokuta ke amfani da tashin hankali wajen sarrafa ayyukan.
Gwamnati da masana’antar hakar ma’adinai na fuskantar asarar ɗaruruwan miliyoyin daloli a duk shekara sakamakon wannan aiki, saboda asarar kuɗaɗen haraji, kuɗaɗen sarauta da kuma kuɗaɗen da za a samu daga sayar da ma’adinan.
Sabon lamarin ya sake jawo hankali kan haɗarin da masu shiga tsoffin wuraren hakar ma’adinai ke fuskanta, musamman wuraren da aka daina amfani da su kuma ba sa bin ka’idojin tsaro na wuraren hakar ma’adinai.
