
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’ummar Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno, sun shiga firgici a jiya Litinin sakamakon fashewar boma-bomai a wurare mabanbanta a birnin, lamarin da ya yu ajalin mutane da dama.
Ana zargin ‘yan ta’addar Boko Haram ne suka dasa ababen fashewar, waɗanda suak tarwatse jim-kaɗan bayan shan ruwa.
Shaidun gani da ido sun ce tashe-tashen boma-boman sun jefa tsoron acikin al’ummar yankunan da ke kusa da waejn da abin ya faru, wanda ya sa da dama suka riƙa ƙaurace wa wuraren da ake fargabar aukuwar wani hari.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, Nahum Daso Kenneth ya tabbatar a faruwar iftila’in a wata takarda da ya fitar, inda ya bayyana cewa hare-haren sun faru ne a Kasuwar Monday Market da ƙofar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, da kuma yankin gadar sama ta Post Office.
Ya ƙara da cewa, jami’an tsaro sun gaggauta isa wuraren tare da killace su, inda jami’an sashen ganowa da kwance boma-bomai suka gudanar da bincike domin tabbatar da babu sauran barazana.
Kazalika, sanarwar ta kuma ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci domin samun kulawa, yayin da jami’an tsaro suka ƙara tsaurara matakan tsaro a Maiduguri da kewayenta domin hana sake faruwar irin wannan lamari.
Wannan al’amari ya auku ne jim-kaɗan bayan mayaƙan Boko Haram sun kai farmaki a sansanin sojoji na Ajilari da ke kewayen Maiduguri.




