Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwamishinan lafiyar jihar Legas Akin Abayomi ya bayyana cewa mutum 10 ne suka kamu da Diphtheria daga ranar 1 ga Janairu zuwa ranar 27 ga Maris.
Bisa ga wani takardar da ya fitar ranar Lahadi Abayomi ya shaida cewa gwamnati ta dauki matakai domin dakile yaduwar cutar a jihar.
Ya ce cutar ta ɓarke a ƙananan hukumomi da dama a jihar amma ƙaramar hukumar Eti-Osa ne da fi fama da yaduwar cutar inda a wurin an samu mutum 44 da ake zargin sun kamu da cutar.
Kwamishinan lafiyan y ace ƙananan hukumomin da suka haɗa da Alimosho, Badagry, Ikorodu, Kosofe, Ojo, Mushin da Lagos Island na daga cikin kananan hukumomin da cutar ya fi yaɗuwa.
Abayomi ya ce an auna sufurin jinin mutum 76 da ake zargin sun kamu da cutar in da sakamakon ya nuna cewa mutum 10 sun kamu, 63 basa sauke da cutar.
“Akwai sakamakon mutum uku din da ake jira wanda aka dauki sufurin jinin su ranar 26 ga Maris.
Ya ce akwai mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar saboda alakar su da makarantar ‘Kings collage’ dake karamar hukumar Eti-Osa, Lagos State Model da Meran dake ƙaramar hukumar Alimosho.
An kuma samu wasu daga suka kamu da cutar a babban asibitin koyarwa na jihar Legas LUTH dake Mushin, makarantar De-Emmaculate, Mile 12 dake karamar hukumar Kosofe da makarantar Gbara dake karamar hukumar Eti-Osa.
“Waɗannan ƙananan hukumomin na daga cikin wuraren da gwamnati za ta bada karfin ta wajen yi wa mutane allurar rigakafi da wayar da kan mutane game da cutar.
“Mutum 21 da suka kamu da cutar sun karbi maganin cutar Diphtheria Antitoɗin (DAT) inda a cikin su akai waɗanda aka gano su daga makarantar Kings collage dake Eti-Osa dake da mutum 14.
“Sauran mutanen da suka karɓi maganin an gano su a makaranta Lagos State Model school, Meiran da wasu wurare dake ƙananan hukumomin Alimosho, Kosofe da Badagry.
Abayomi y ace duk waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar an killace su domin tabbatar da sun samu kulan da ya kamata sannan da ganin an hana su yada cutar.
Ya yi kira ga mutane da su haɗa hannu da jami’an lafiya domin tabbatar da daƙile yaɗuwar cutar.
Abayomi ya ce yaɗuwar cutar ya fara daga mako na uku, huɗu da goma na 2025 inda akan samu mutum hudu da suka kamu da cutar a cikin kowani mako.
“An fara samu ragowar yaduwar cutar a cikin makonin da suka gabata inda hakan ke nuni da cewa matakan daƙile yaɗuwar cutar na aiki sannan akai yiwuwar samun nasarar daƙile yaɗuwar cutar idan haka aka mai da hankali wa ci gaba da ɗaukan matakan.
“Gwamnati ta fara gudanar da bincike domin gano mutanen da suka kamu da cutar inda zuwa yanzu ta gano mutum 118 inda mutum 100 ta kamala tattance su sannan bata kamala na sauran mutum 18 ba.
“Mutum 36 dake zama a kananan hukumomin da cutar ya barke sun yi allurar rigakafin cutar na prophylaɗis.
Abayomi ya ce gwamnati ta ci gaba da yi wa mutane allurar rigakafin cutar inda jami’an lafiya, mutanen da suke tare da wadanda suka kamu da cutar na daga cikin wadanda aka yi musu allurar rigakafin.
Ya ce tun bayan bullowar cutar gwamnati ta yi wa mutum 36,310 allurar rigakafin cutar.
Kwamishinan lafiyan ya ce mutum7,473 masu shekaru 9 zuwa 17, 28,837 masu shekaru 18 zuwa sama da jami’an lafiya 13,633 na daga cikin yawan mutanen da suka yi allurar rigakafin cutar a jihar.
Ya ce gwamnmati za ta ci gaba da yi wayar da kan mutane game da citar tare da jadadda kiyaye matakan samun kariya daga kamuwa da cutar.
