Tinubu ya faɗi dalilan cire asusun Abuja daga tsarin baiɗaya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban ƙasa Bola Tinubu a ranar Lahadi a Abuja ya ce, gwamnatinsa ta cire asusun kula da birnin tarayya Abuja daga asusun baiɗaya ne, domin samar da cigaban mai sauri ga mazauna birnin tarayyar da ba su damar shiga a dama da su wajen jagoranci.

Shugaban, wanda ya karɓi baƙuncin mazauna birnin tarayyar a gidan gwamnati da ke Abuja waɗanda suka je yi wa Shugaba Tinubu barka da sallah, ya ce, sanya hukumar kula da birnin tarayya cikin asusun na jawo mata koma baya wajen samar da abubuwan more rayuwa a birnin da ya sa ba a ganin wani cigaba.

Mutanen da suka je yi wa shugaban ƙasa barka da sallah, sun je ne a ƙarƙashin jagorancin ministan Abuja, Nyesom Wike.

Shugaba Tinubu ya nuna cewa ‘yantar da hukumar daga shiga asusun baiɗayan ya haifar da cigaban da ake buƙata cikin sauri da bunƙasa kiwon lafiya da inganta tsaro.

“Zan iya tunawa cewa, ministan Abuja ya zo ya same ni tare da roƙona na cire hukumar daga asusun baiɗaya domin samun damar gudanar da aiki sosai. Nuna min abin da kake so ka cimma. Daga nan ne ya bayyana min tunaninsa da kuma abin da yake fata,” inji Tinubu.

“Daga nan ne komai ya fara sauyawa. Na fara ganin ana raya ƙauyuka da ke babban birnin tarayya, da farfaɗo da ayyukan da aka yi watsi da su da kammala aikin ginin gidan mataimakin shugaban ƙasa da aka yi watsi da shi na tsawon lokaci da inganta harkar lafiya da inganta ilimi ga yara da zuba musu kujerun zama.”

Shugaba Tinubu ya yaba wa ministan Abuja saboda tabbatar masa da cewa ‘yantar da hukumar da ya yi abu ne da ake iya gani wajen yadda yake sauya fasalin Abuja da ba wa ma’aikatan gwamnati damar neman dagewa don samun cigaba.

“Kai ne ka ba mu dalilin da ya sa muke da bakin magana, idan ba don kawo cigaban da kai ba, sai dai mu yi shiru. A yanzu za mu iya yin murnar cigaban da kawo wa garin Abuja,” in ji Tinubu.

Shugaba Tinubu ya kuma ƙarfafa wa mazauna birnin tarayya Abuja da sauran masu ruwa da tsaki da kaucewa na nuna bambanci na addini da ƙabilanci a cikin jagorancinsu, a maimakon haka su mai da hankali ga cimma sakamakon da ya kamata.

“A yau, muna zaune cikin zaman lafiya da ingantuwar tsaro. Ana samun raguwar masu fama da yunwa. Farashin abinci na raguwa. Za mu iya tafiya kasuwa mu yi kasuwancinmu. Sannan bambance-bambancen da ke tsakaninmu na ƙara zama ƙarfi a maimakon rauni.”

“Wannan aiki ba wai na Wike ba ne ko nawa, aiki ne na kowa da kowa. Nyesom Wike yana ta ƙara tabbatar da basirarsa wajen kawo abubuwa daban-daban. Yana ta ƙoƙarin nuna mana mu zuri’a ɗaya ce da ke zaune a gida ɗaya amma a mabambantan ɗakuna a ƙarƙashin inuwa ɗaya”

Daga nan ne shugaba Tinubu ya nemi al’umma su nuna juriya da faɗaɗa tunaninsu da nuna kishin ƙasa.

Shi ma ministan Abuja ya gode wa shugaban ƙasa kan yadda ya yi musu maraba a gidan gwamnati.

“Wannan wani tarihi ne aka kafa na yadda mazauna Abuja da kansu suka samu damar miƙo maka gaisuwa da kansu a irin wannan lokaci mai albarka. Mun yi farin ciki sosai.”

Wike ya yi alƙawarin cigaba da mara wa shugaban ƙasa baya da himmatuwa wajen bunƙasa babbar birnin tarayya. Ya ba shi tabbaicn cewa nan ba da daɗewa ba za a kammala sauran ayyukan.

“Duk da bambance-bambancen da ke tsakaninmu, mun haɗu waje ɗaya domin mara wa gwamnatinka baya da sabunta fatan al’umma,” in ji Wike.

Sauran waɗanda suka samu halartar taron sun haɗa da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da mashawarci na musamman ga shugaban ƙasa kan tsaro, Nuhu Ribadu, da ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris.

Sauran sun haɗa da mambobi hukumar babban birnin tarayya Abuja da ‘yan majalisu da ma’aikatan shari’a da malaman addini da shugabannin gargajiya da jami’an tsaro da ƙungiyoyin mata da matasa.

By ukarofi