Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Yaƙi da Rashawa da Sauran Manyan Laifuka (ICPC) za ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan shirin bin gaskiya wajen kashe dukiyar al’umma da Hana Rashawa a ƙananan Hukumomi mai taken (ACPP-LG) a faɗin ƙasar.
Wannan shiri yana da nufin inganta tafiyar da kuɗi, nuna gaskiya, da kuma fallasa bayanai a matakin ƙananan hukumomi.
Mai magana da yawun ICPC, Demola Bakare, ya bayyana a wata sanarwa a ranar Laraba cewa, ICPC ta daɗe tana haɗa gwiwa da al’ummomin yankunan karkara ta hanyoyin shirye-shiryen ƙananan hukumomi daban-daban.
“Waɗannan ƙoƙari ba wai kawai sun zama dandali na ilmantarwa da wayar da kai ba, har ma sun ba wa ‘yan ƙasa ikon gano da kuma kai rahoton ayyukan rashawa,” inji Bakare.
