Ina neman haɗin kan matasan Giwa don gudanar da jagoranci nagari – Kwamared Alkurkawee

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar Matasan Nijeriya (NYCN) reshen ƙaramar Hukumar Giwa, Kwamared Nuhu Haruna Alkurkawee, ya nemi haɗi kai da goyon bayan matasan ƙaramar hukumar don gudanar da jagoranci nagari a tsakanin matasan yankin.

Kwamared Alkurkawee ya bayyana hakan ne a cikin wata zantawa da ya yi da wakilinmu ta wayar tarho jiya Alhamis.

Ya bayyana cewa wannan matsayi na shugabancin matasan ƙaramar Hukumar Giwa da yake jagoranta wani nauyi ne da Allah Ya ɗora masa, inda kuma ya ƙara da cewa matasa ne ‘yan uwansa suka ga cancantarsa da kyakkyawar mu’amalarsa da matasa da jagororin yankin suka zaɓe shi, inda ya ƙara da cewa duk wanda yake ja da hukuncin Ubangiji yana tare da baƙin ciki a rayuwarsa.

“Allah ne ya ba ni wannan matsayi, ba iyawata ko dabarata ba ce. Saboda haka duk mai ja da ikon Allah wannan shi zai wahala,” inji shi.

Kwamared Alkurkawee ya yi amfani da damar wajen yaba Shugaban ƙaramar Giwa, Hon. Ahmad Sama’ila Yakawada musamman yadda ya fara ayyukan raya ƙasa da gina al’ummar yankin, tare kuma da jawo matasa a jiki don cin gajiyar gwamnatinsa.

Ya kuma yaba wa Gwamna Uba Sani musamman yadda ya karkata aiwatar da ayyuka a karkara wajen samar musu da romon dimukraɗiyya.

A ƙarshe, Kwamared Alkurkawee ya shawarci matasan ƙaramar hukumar da jihar Kaduna bakiɗaya da su zama jakadu nagari waɗanda za a yi alfahari da su a kodayaushe.

Har yanzu dai wasu daga cikin tsoffin shugabannin kungiyar reshen ƙaramar hukumar Giwa suna iƙirarin su ne shugabannin ƙungiyar duk da zaɓen da aka gudanar a kwanakin baya, wanda shugaban ƙaramar hukumar ya miƙa musu takardar shaidar fara aiki.

By ukarofi