Sojojin Nijar sun ci gaba da tsare Bazoum amma sun saki ministocinsa

Spread the love

Shugabannin sojojin mulkin Nijar sun saki fursunoni sama da 50 da suka haɗa da tsoffin ministocin gwamnatin da suka hamɓarar a shekarar 2023. Daga ciki akwai tsoffin ministocin tsaro, man fetur da na kuɗi, da kuma wasu manyan hafsoshin sojin ƙasar, waɗanda aka kama ko aka zarge su da laifin kitsa juyin mulkin da aka yi a baya.

Hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum, wanda ake tsare da shi tun bayan da sojoji suka ƙwace mulki a shekarar 2023, baya cikin jerin waɗanda aka sako duk da kiran da ƙasashen duniya suka yi na a sako shi.

A lokacin da BBC ta yi tambaya game da ci gaba da tsare shugaba Bazoum, ministan shari’a Aliliyou Daouda ya yi tsokaci game da “tsaron ƙasa da ikon mallakar kasa.”

Ministan shari’a Aliliyou Daouda ya shaida wa BBC cewa, “Batun sakin nasa lamari ne na cikin gida a Nijar kuma ya shafi Nijar ne kawai.”

Ana zargin Bazoum da zagon ƙasa ga tsaron ƙasa da kuma cin amanar ƙasa.

Sakin sauran na daga cikin shawarwarin taron ƙasa da aka gudanar a watan Fabrairu, tare da tsawaita wa’adin mulkin Janar Abdourahamane Tiani da shekaru biyar.

An kama ministocin da jami’an suka saka ne bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yulin 2023 wanda ya kawo Janar Tchiani kan karagar mulki, kuma ana tsare da su ne bisa zargin haɗa baki da zagon ƙasa ga harkokin tsaro da hukumomin jihar.

Wannan mataki dai na iya zama wani yunƙuri da gwamnatin mulkin soji ke yi na sasanta ƙasar da kuma samun goyon bayan jama’a.

An yi irin wannan afuwa daga gwamnatocin sojoji a Burkina Faso da Guinea.

Tun bayan kwace mulki, gwamnatin Janar Tchiani ta ƙarfafa alaƙa da Rasha tare da yanke hulɗa da Faransa.

Haka kuma ta buƙaci tsohuwar gwamnatin mulkin mallaka da ta janye sansanonin sojinta daga ƙasar.

Dangantakar Nijar ta yi tsami da makwabtanta. Tare da Mali da Burkina Faso, inda sojoji suka ƙwace mulki, tare da janyewa daga ƙungiyar Ecowas ta yammacin Afirka.

By ukarofi