Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano
Habiba Isa Dorayi da aka fi sani da Habiba Dorayi matashiya ce da ta taso a masanaantar fim ta Kannywood. A tattaunawar ta da Ibrahim Hamisu, a Kano, za ku ji cikakken tarihinta da kuma yadda frodusoshi suke ribibin saka ta a fim, ku biyo mu:
MANHAJ: Za mu so ki gabatar mana da kanki?
HABIBA ƊORAYI: Sunana Habiba Isah, an fi sani na da Habiba Dorayi.
Ko za ki ba mu taƙaitaccen tarihinki?
An haife ni a Rano. Da kakanina suka rasu sai muka dawo cikin garin Kano. Na yi Primary, na yi secondry, iya nan na tsaya.
Me ya baki sha’awa ki ka shiga masana’antar fim ta Kannywood?
A gaskiya na daɗe ina sha’awar fim, kuma ina kallonsa a matsayin sana’a ce mai kyau.
Yaushe ki ka fara sha’awar shiga harkar Kannywood?
Ai gaskiya tun ina ƙarama na ke sha’awar fim, domin a lokacin da na ke yarinya ko aike na a ka yi na ga gidan ana kallo to sai na tsaya na kalla, to a haka na ke to amma da na girma abin ya fi shiga raina.
To yaushe ki ka shiga masana’antar fim ta Kannywood?
Ban daɗe ba gaskiya, domin ban fi shekara biyu da shigowa ba.
Da wane fim ki ka fara?
Ba da fim na fara ba gaskiya, na fara ne da waƙoƙin siyasa na background, sai yanzu ne na fara yin fim ɗin kaɗan-kaɗan haka.
Ya zuwa yanzu kin yi waƙoƙin siyasar kamar nawa?
Za su iya kaiwa goma sha uku.
To da wane fim ki ka fara?
Na fara ne da bidiyo na waƙa, inda muka yi na wata ƙungiyar tallafa wa ilimin mata a Jihar Katsina, to a waqar ne na ganni ga ni a bidiyo ƙiriƙiri. To daga nan sai na fara da wani fim mai suna ‘Haɗarin So’ da shi na fara a finafinai.
Ya zuwa yanzu kin yi finafinai za su kai nawa?
Ban yi da yawa ba, domin ba su fi bakwai ba, waɗanda suka haɗa da ‘Haɗarin So’ da ‘Haidar’ da sauransu.
Kafin ki shigo an yi maki kantawaye ne?
Gaskiya ni ba a min ba, kuma ban ga an yi min na, kuma ni abinda na sani shi ne, ana duba ƙwarewarka ne sannan a sanyaka a aiki, kasan ba zai yiwu ba ba ka goge ba ko kana da kurakurai a sakaka a aiki ba.
Waɗanne irin nasarori za ki iya cewa kin samu daga shigarki zuwa yanzu?
Mun gode Allah, zan iya cewa na samu nasarori, domin idan na je wani aiki sai ka ga an kiraka wani wajen, akwai wata rana da na je wani aiki zan yi scene ɗaya, to da wani ya ganni ya kirani ya sakani a fim ɗin sa, to sai da na yi scene ya kai 30, ka ga wannan ma nasara ce. Kuma bayan haka ana kirana daidai gwargwado.
Daga shigowar ki Kannywood zuwa yanzu akwai ƙalubale ne ko babu?
Gaskiya ya zuwa yanzu dai ban samu wani ƙalubale ba, kuma ba na fata, duk da yake ɗan adam ba a raba shi da jarrabawa ba.
Shin wane ne mai gidanki a Kannywood?
Dariya! Ai ni kam kowa ma ubangina ne duk wanda ya kira ni ya sakani a fim ɗinsa maigidana ne, domin sana’a ce, don haka kowa mai gidana ne.
Wane ne ya fara sakaki a fim?
Abdulaziz Dan Small ne ya fara saka ni a fim.
Daga cikin finafinan ki wanne ne ya fi burgrki?
Gaskiya dukkanninsu ina son su, domin dukkansu an ba ni roll mai kyau.
Wane fim ne ya ba ki wahala kafin ki yi shi?
Fim ɗin ‘Haidar’ shi ne ya ba ni wahala, domin na jima ina maimaita abu ɗaya, sai da daraktan ya yi min tsawa sannan na samu na yi yadda ake buƙata.
Menene burinki a Kannywood?
Burina shi ne na yi finafinai masu yawa, na yi fice na fi haka a wannan masana’anta tamu ta Kannywood, duk da yake neman halal ba a samun shi da sauƙi.

Ya batun aure fa?
Ban tava yi ba, kuma insha Allah zan yi.
Yaushe ki ke sa ran za ki yi auren?
Da na cika wancan burin nawa da na ambata zan yi aure, kai ko burin bai cika ba, da zarar na samu wanda ya kwanta min a rai zan yi aure.
To yanzu akwai wani lamba ɗaya ne da ki ke jin za a yi da shi ne?
Dariya! Babu, gaskiya babu.
To yanzu idan wani ya zo za ki iya ajiye fim ki aure shi?
Sosai kuwa, amma idan ya kwanta min, na ji ina sonsa to zan aure shi.
Daga ƙarshe me za ki ce ga abokan sana’arki da masoyanki?
Ina yi masu fatan alheri, ni ma ina yi wa kaina fatan alheri.
Mun gode.
Ni ma na gode sosai.
